Duk da cewa APC ta yi tir da kashe-kashen da suka fusata Kiristoci har suka fito yin tattakin lumana domin nuna damuwar su a fili, APC ta ce har yanzu Gwamnatin Shuhaba Muhammadu Buhari ta na matukar kokari kuma ta yi rawar gani sosai wajen dakile Boko Haram da sauran hare-hare da kashe-kashen da ake fama da su a kasar nan.
“An zabi Shugaba Buhari a 2015, bayan ya hau ya yi matukar kokari. Wannan kokarin wajen dakile ta’addanci da sauran rikice-rikce ne ya sa aka sake zaben sa cikin 2019.
“Duk da dai har yanzu ana samun ‘yan hare-haren ta’adanci nan da can, musamman na sari-ka-noke a inda babu wadatar hakan bai dusashen gagarimar nasarar dakile Boko Haram da wannan gwamnati ta yi ba.
“Kada mu yarda mu bada kai ga borin ‘yan ta’adda, masu kokarin yin amfani da haddasa rudu a tsakanin mabiya addinai domin su hada mu fada da juna.
“Dan ta’adda babu ruwan sa ta batun addinin wadanda ya ke so ya kawar ko ya kai wa harin ta’addanci. Babu ruwan sa da addini ko siyasar jama’a. Babu ruwan sa da tantancewa. Don haka ta’addanci gaba ya ke yi da mu gaba daya. Wajibin mu ne mu hada hannu domin karasa murkushe su.”
APC ta yi kiran cewa ya kamata shugabannin addinai su rika kai zuciya nesa, a rika sani da kuma tauna irin maganar da za a fitar, domin ita magana zarar-bunu ce.
Daga nan kuma jam’iyya mai mulki ta bugi kirjin cewa Gwamnatin Buhari ta yi rawar gani, domin a yanzu babu wani yanki ko da inci daya da ke hannun Boko Haram.