ZANGA-ZANGAR KIRISTOCI: APC ta maida wa CAN martani

0

Jam’iyyar APC ta maida kakkausan martani dangane da tattakin lumanar da Kiristoci suka yi a sassan kasar nan, a ranar Lahadi a bisa umarnin Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN).

APC ta ce kalaman da suka rika biyo bayan zanga-zangar daga bakin CAN “ya nuna cewa kungiyar tq dunka rigar siyasar-addini ta makala, ta yadda ta ke yi wa Boko Haram wani kallo da kuma gurguwar fahimtar rashin amfani da kaifin tunani.”

APC ta kara cewa hare-hare da kashe-kashen da Boko Haram ke yi kwanan nan, su na yi ne domin su hada Kiristoci da Musulmai fada. Don haka abin takaici ne wasu da ake kallon manya ne a kasar nan har za su rika amfani da tashe-tashen hankulan su na yanko maganganu babu kimtsi babu tunani.”

Zanga-zangar Lumanar Nuna Damuwa

Dukkan alamu sun tabbatar da cewa kiran da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa, CAN, Samson Ayokunle ya yi cewa a fito a yi zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadin yadda ake kashe-kashe, ya samu karbuwa a kasar nan.

Dubun dubatar Kiristoci sun fito a safiyar Lahadi su na zanga-zanga tare da yin addu’o’i kan titi nan Lagos, a karkashin jagorancin Shugaban Cocin RCCG, Fasto Enoch Adebayo domin nuna rashin jin dadin yadda ake ci gaba da kashe-kashe a fadin kasar nan.

Wannan jerin-gwano dai sun gudanar da shi ne domin nuna wa gwamnati rashin jin dadin abin da suka kira sakaci da gwamnatin ke yi wajen fannin tsaro.

Hususan an shirya jerin gwanon ne a garuruwa, domin nuna bacin rai a kan yadda Boko Haram suka kama Shugaban Kungiyar Kiristoci na Jihar Adamawa, Lawan Andimi ta yanka shi, sannan ta watsa bidiyon yadda al’amarin ya faru.

Cikin makonnin nan biyu da wuce, rahotanni sun nuna cewa an kashe daidaikun Kiristoci a jihohin Adamawa, Barno da Kaduna.

Cikin jawabin da Shugaban CAN na Kasa ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya ce ya bada umarnin yin tattakin ne domin a nuna wa gwamnati gazawar ta, tare kuma da yin kira ga gwamnatin ta farka daga minsharin da ta ke yi wajen yin sako-sako da harkar tsaro.

“Mu na kira ga Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen dukkan ‘yan Boko Haram da ke tsare, sannan mu na kira ta tsaida kashe kashen Kiristoci da ake yi a Kudancin Kaduna, Adamawa, Taraba da Barno da sauran yankunan kasar nan.

Kisan wani dalibin Jami’ar Maiduguri da Boko Haram suka yi, a kan hanyar sa ta shiga jami’ar daga Jos, kwanaki kadan bayan kisan shugaban CAN na Adamawa, ya harzuka Kiristoci sosai a Arewacin kasan.

Ana ci gaba da kiraye-kirayen cewa Manyan Hafsoshin sojojin kasar nan su sauka, domin a samu sabbin da za su iya dakile Boko Haram da hare-haren masu garkuwa da mutane.

Ranar Alhamis Sanata Elisha Agba ya mike a Majalisar Dattawa ya bayyana yadda ya ce Boko Haram sun shiga yankunan Michika da Madagali sau bakwai a cikin watanni biyu kadai.

Share.

game da Author