ZAMFARA: Shugaban karamar hukumar Tsafe ya koma PDP

0

Shugaban karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara, Aminu Mudi ya canja sheka daga APC zuwa PDP.

Aminu ya koma PDP tare da Kansiloln sa 10.

” Babban dalilin da ya sa muka koma jam’iyyar PDP shine ganin yadda gwamnan jihar Bello Matawalle ke zuba aiki a jihar. Baya ga haka da kokarin da yayi wajen dawo da zaman lafiya a jihar.

” Wadannan suna muhimman dalilan da ya sa muka ga ya kamata mu bi shi gaba dayan mu domin samun ci gaba a jihar.”

Daya ke karbar masu canja sheka, gwamna Matawalle ya yabawa shugaban karamar hukumar inda ya ce kofar jam’iyyar PDP a bude take ga duk wanda zai shigo ta sannan zai ci gaba aiki tukuru don ganin mutanen jihar sun kwankwadi romon dimokradiyya sun cika ciki fam a wannan zamani na mulkin sa.

Baya ga haka kuma ya nada tsohon mataimakin sufeton ‘yan sanda Mamman Tsafe Mai bashi sharawa kan harkokin tsaro.

Gwamna Matawalla, ya zama gogarma, kuma abin yabo ga mutanen jihar Zamfara inda tun bayan zaman sa gwamnan jihar ya maida hanakali wajen ganin an samu dawowar zaman lafiya na dindindin a jihar.

Mutane ba a jihar ba kadai harda wasu jihohin suna yaba wa gwamna matawalle sannan harda wasu gwamnonin sun fara koyi da yadda yake tunkarar hare-ahren ‘yan ta’adda da salon samar da zaman lafiya da ya runguma.

Share.

game da Author