Likitan koda dake aiki a asibitin jami’ar Virginia a kasar Amurka Rasheed Balogun ya bayyana cewa zafin rana na haddasa ciwon koda musamma ga matasa.
Balogun ya fadi haka ne a taron likitocin koda na Najeriya karo na 32 da aka yi a gaein Ibadan ranar Laraba.
Ya ce ya gano haka ne daga sakamakon binciken da wasu likitoci suka yi a baya da sakamakon binciken da shi ya gudanar.
“ Na gudanar da wannan bincike ne domin gano dalilin da ya sa matasa masu koshin lafiya ke yawan kamuwa da ciwon.
“A yanzu haka bincike ya nuna cewa ciwon ya yi ajalin matasa 240,000 a kasar Amurka.
Balogun ya kuma ce sakamakon binciken da ya yi ya kara nuna masa cewa manoma da birkiloli ne suka fi kamuwa da wannan ciwon.
“ Hakan na da nasaba da yawan daukan lokaci da suke yi a karkashin rana sannan da dama a cikin su basa shan ruwa domin rage zafin dake shiga jikin su.
“Akwai kuma yiwuwar cewa manoma ne suka fi yawan kamuwa da wannan ciwo a dalilin shakar maganin feshin da ake amfani da shi a gonaki.
Ya yi kira ga mutane musamman ma’aikata irin haka da su rage yawan zama a karkashin rana suna aiki cewa yin haka na cutar da kiwon lafiyar su.
“Ina kuma kira ga masu daukan mutane aikin birkila da noma da su rika bari ma’aikatan su na samun wurin hutawa tare da karfafa gwiwowin su kan mahimmancin shan ruwa a kowani lokaci domin guje wa kamuwa da wannan ciwo.
“Ya kuma kamata mutane su yawaita shan ruwa musamman a lokacin zafi domin rashin shan ruwa na cikin hanyoyin kamuwa da ciwo.
Balogun ya yi kira ga gwamnati da ta tsaro hanyoyin samar da makamashin girki da ake amfani da su a Najeriya cewa girki da itace, gawayi da sauran suna daga cikin abubuwan dake kawo canjin yanayi a kasar nan.
Ciwon koda na kama mutum ne idan hanyar da koda ke amfani da shi wajen fitar da fitsari ya toshe.
Alamomin kamuwa da ciwon sun hada da yawan yin ciwon kai, kumburin jiki musamman kafafuwa,ciwon ciki da sauran su.
Bincike ya nuna cewa kashi 20 zuwa 30 bisa 100 na mata na yawan kamuwa da ciwon koda.
Hanyoyi 12 da ake iya kamuwa da ciwon.
1. Hawan Jini.
2. Zubar/cire ciki.
3. Kamuwa da cutar ‘Fibroid’.
4. Cutar dajin dake kama mahaifa.
5. Kamuwa da cutar siga.
6. Ana iya gadon cutar.
7. Kamuwa da cutar sanyi na kowo cutar.
8. Samun rauni a koda na kawo cutar.
9. Rashin shan maganin kawar da cutar hawan jini, zazzabin cizon sauro, kanjamau duk na iya kawo cutar.
10. Rashin motsa jiki da cin kayan abincin dake inganta kiwon lafiya na sa a kamu da cutar.
11. Rage yawan cin gishiri musamman danyen gishiri a abinci
12. Yawan shan magunguna musamman ba tare da izinin likita ba.