Ibrahim da aka kada a zaben soyayya da aka yi a garin Giade, Jihar Bauchi ya bayyana cewa zai garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben.
Idan ba a manta ba, wata budurwa mai suna Khadija ta umarci ‘yan gari su zaba mata miji cikin wasu mazaje biyu Ibrahim da Inusa.
Manyan gari suka shirya wannan zabe kuma mutane sun fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’un su.
Bayan an kammala zabe an kuma kirga, sai Inusa yayi nasara.
Sai dai kuma tun bayan bayyana sakamakon zaben wanda ita kanta Khadija ta halarci wajen zaben, abokin takarar Inusa, wato Ibrahim ya yi korafin an tafka magudi a zaben.
A bisa wannan dalilai, Ibrahim ya ce lallai zai garzaya kotu domin abi masa hakkin sa na samun soyayyar masoyiyar sa wato Khadija.
Tuni dai gar an mika wa Inusa shaidar nasara a zaben kuma Khadija ta yi murnar haka har ta dauki hotuna da shi.
Discussion about this post