Kotun Koli a ranar Larabar nan ta yi fatali da rokon da jam’iyyar APC ta yi, inda ta nemi kotun ta maida David Lyon da tsige a matsayin zababben gwamnan Bayelsa.
A cikin wani hukunci da alkalai bakwai duk suka taru suka amince, a karkashin Babban Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, sun ce rokon da APC da kuma dan takarar ta Lyon suka yi ba shi da madogara, domin tuni ma an soke dukkan kuri’un da aka jefa masa.
Sannan kuma Kotun Koli ta ce ba ta da hurumin da za ta warware hukuncin da ita da kan ta ta yanke, a matsayin ta na Kotun Koli.
Da ta ke karanto sakamakon hukuncin da Kotun Koli din ta yanke, Babbar Mai Shari’a Amina Augie, a cikin fushi ta bayyana cewa, “Babu wani mai karfi a duk duniyar nan da zai iya tirsasa Kotun Koli ta canja hukuncin da ita da kan ta ta rigaya ta yanke.”
Daga nan kuma Augie ta ce APC da dan takarar ta Lyon za su biyar ladar bata wa PDP, sabon gwamna Diri da mataimakin sa lokaci da suka yi har ta naira milyan 10.
Tun bayan da PDP ta koma kotu neman sake bibiyar hukuncin zaben gwamnan Imo, wanda ta yi korafin cewa Kotun Koli ta yi ruwan kuri’u ga Hope Uzodinma na APC, Fiye ma da adadin kuri’un da ke da rajista, sai ita kuma APC ta koma Kotun Koli ta na so a sake maida mata kujerar gwamnan Bayelsa, wadda Kotun Koli ta kwace ta bai wa dan takarar PDP.
Bayan yanke hukuncin da aka kwace kujerar gwamnan Bayelsa daga APC aka bai wa PDP, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Jama’iyyar PDP ta gargadi Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya daina saka bakin sa a cikin hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan zaben gwamnan Jihar Bayelsa.
PDP ta ce kalaman da Oshiomhole ya yi bayan an kwace kujerar gwamna daga hannun dan takarar APC an bai wan a PDP, ganganci ne, kuma kasassaba ce, wadda mai hankali bai kamata ya yi ta ba.
Oshiomhole dai ya yi barazanar cewa kada a sake a rantsar da dan takarar PDP wanda Kotun Koli ta maida wa nasarar zaben.
Bayan an rantsar da shi kuma sai APC ta koma Kotun Koli, domin neman a maida mata kujerar ta.
Wannan rokon ne ita Kotun Koli ta yi fatali da shi a yanzu.