ZABEN 2023: Kungiyar Dattawan Arewa ta gindaya sharuddan irin shugabannin da za a zaba

0

Kungiyar Dattawan Arewa mai suna Northern Elders Forum, ta bayyana cewa idan a zaben 2023 mai zuwa, kada ‘yan Arewa su zabi kowa sai shugabannin da aka gamsu da cewa lallai su na da kishin shiga gaba domin su ceto yankin daga tabarbarewa.

Jagoran kungiyar Ango Abdullahi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Zaria, Jihar Kaduna.

“Mun lura cewa an fara kulla kutunguila da kisisinar siyasar zaben 2023, ta hanyar neman yin amfani da Arewa domin a cimma manufar siyasa.

“To mu na jan hankali da babbar murya cewa Arewa ba za ta zabi kowane ‘kwaram da hama’, sai wanda lallai aka gamsu cewa su na da kishin ci gaba, ba kishin kan su kadai ba.

“Arewa na da bukatarta a siyasa, kuma sai wadanda aka san zai biya mata wannan bukatar kadai za a zaba.

Da ya juya kan matsalar tsaro, Abdullahi ya yi kira a yi amfani da zakakurai masu kishi tsantsa wajen ganin an yi wa wannan matsala kwaf-daya, an magance ta.

Da ya ke magana a kan Boko Haram, ya yi kira ga shugabannin addinai su hankalin mabiyan su, kada Boko Haram su hada Musulmi da Kirista fada a kasar nan.

“Mun yi tir da yadda Boko Haram ke tsamen Kiristoci su na kashe su, wanda wani shiri ne kawai domin su hada mabiyan addini biyu fada a kasar nan.

“Haka kuma mun kara yin Allah-wadai da yadda ake kashe Musulmi da Kiristoci a hare-hare daban-daban a ‘yan ta’adda ke kaiwa.

Ya yi kira a hada kai a kasar nan domin a magance kalubalen da ke fuskantar kasar baki daya. Sannan kuma ya ce ya na maraba da kowace kungiya mai neman a zauna domin tattauna yadda za a fita daga cikin maquyacin halin da Najeriya ke ciki.

Share.

game da Author