Ma’aikatar Ayyukan Jinkai, Agaji da Inganta Ruyuwa, ta bada sanarwar yin wani gagarimin shiri da za ta bijiro da shi domin kawar da duk wani cikas, nakasu da waskiya da kudaden da ke faruwa a cikin ahirye-shiryen inganta rayuwar jama’a a kasar nan, wato SIP.
Cikin wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar, a karkashin Mataimakiyar Daraktar Yada Labarai, Rhoda Iliya, ta ce wannan aikin tankade da rairaya zai shafi dukkan shirye-shiryen SIP da suka hada da N-Power, Ciyar da ‘Yan Makaranta da kuma Tura Tallafin Kai-tsaye a Asusun Fakirai.
Ta ce a kokarin da wannan gwamnati ke yi wajen ganin an rika kashe kudaden gwamnati yadda ya dace, za a yi sabon tsarin kashe kudade a Africa tsare-tsaren inganta rayuwar al’umma (SIP), domin a rika tabbatarwa ana kashe kudaden yadda suka kamata.
Sannan kuma za a rika tabbatar da cewa kudaden na zuwa aljifan wadanda suka kamata su amfana da su.
Hukumar ta koka dangane da yadda wasu masu aikin gudanar da tasarifin kudaden wasu shirye-shiryen ke sa shiriritar karkatar da kudaden zuwa aljifan su.
Ta ce idan aka sabunta tsarin, za a toshe duk wata kofar almundahana musamman daga masu cin rabo ko ladar aikin da ake biyan su, sannan kuma su rika danna rabon wasu a cikin aljifan su.
Sanarwar ta kara da cewa jama’a sai sun yi hakurin dan tsaukon da za a fuskanta yayin binciken yadda ake hana-ruwa-gudu, da kuma yadda za a bude hanyar ruwan wadda wasu ke ta kokarin rufewa domin amfanar kan su da hakkokin wasu.
Idan aka yi sabon tsarin, Rhoda ta ce zai samar wa gwamnati saukin sa-ido ta ga yadda ake tafiyar da kowace naira daya da aka tanadar wa shirye-shiryen.
Sai dai kuma ta ja hankalin masu cin moriyar shirin cewa kada su bayar da kofa har su rika fifowa soshiyal midiya da jaridu su na rubuce-rubucen batunci a akan tsaikon da wannan kwaskwarima da za a yi wa shirin za ta haifar.
Idan ba a manta ba, kwanan baya wata uwar-tuwo ta tsere da kudaden dafa wa dalibai abincin ciyarwa.
Sannan kuma cikin watan Yuli, 2019, Premium Times ta yi labarin yadda aka kori matasa 2,525, wadanda aka gano ba su zuwa wurin aikin su.