YAR FARA TA NUNA: ASD bai tura kudi asusun ajiyar Shehu Sani ba – Masu Bada Shaida

0

A ci gaba da shari’ar gurafanar da sanata Shehu Sani da EFCC ta yi, kan zargin karbar wasu kudade daga hannun Sani Dauda, wanda aka fi sani da ASD Motors, masu bada shaida sun karyata EFCC a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja.

Masu bada shaidar wadanda ma’aikatan banki ne, EFCC din ce ta gabatar da su. Amma sun shaida wa Mai Shari’a cewa ba su da wani rekod mai suna cewa ASD Motors ya tura wa Shehu Sani kudi a asusun ajiyar bankin su da Sani ke a jiyar kudin sa a ciki.

Mai bada shaidar mai suna Beckley Ojo da Elizabeth Nwoka, wadanda ma’aikatan Guaranty Trust Bank (GTB) ne, dukkan su EFCC din ce ta gabatar da su a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo.

Rahoto ya nuna cewa ya gabatar wa kotu da takardun da ya shaida mata cewa su ne shaidar da ke nuna yadda aka tura kudi daga asusun ASD Motors zuwa ga wasu mutane.

To amma bai bayyana ko shaida yadda aka tura kudin ga Sani ba. Wato ya kasa nuna wa kotu tabbas idan Sanin a cikin wadanda aka tura wa kudaden.

EFCC dai ta na zargin Sani ya karbi kudi dala milyan 25 a madadin Shugaban Riko na EFCC, Ibrahim Magu.

Akwai kuma wani cajin da ake yi masa na karbar kudaden domin ya kai wa Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammad.

Ann kama a ranar 31 Ga Disamba, 2019, inda a ranar 2 Ga Janairu kuma, EFCC din ta garzaya kotu ta karbo iznin ci gaba da tsare shi karin wasu kwanaki 14, domin ta karasa bincike.

Daga baya Ekwo ya bayar da belin sa, inda tun kafin beli Sani ya sha fadar cewa sharri da kazafi da tuggu da siyasa ce ake kulla masa, wadanda ba kuma za su yi galaba a kan sa ba.

Yayin da mai gabatar da kara, Abba Mohammed ya gabatar da ma’aikatan GTB, ta farko ta yi bayanin yadda ASD Motors ya tura naira milyan 3 a asusun wani mai suna Sheriff Shanono, a ranar 2 Ga Disamba, 2019.

Lauyan Shehu Sani mai suna Abdul Ibrahim, ya tambaye ta ko sunan Sheriff Ibrahim daya ne da sunan Shehu Sani? Sai ta ce ita dai ba ta sani ba.

An dai daga kara zuwa Laraba, bayan mai shaida ta biyu ta bayyana yadda ASD Motors ya tura kudi naira milyan 5 a ranar 20 Ga Nuwamba, 2019, a wani asusu, wanda shi ma ba sunan Shehu Sani ba ne.

Share.

game da Author