Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya ce ‘yan ta’adda na shiga soshiyal midiya su na dauka da yin rajistar sabbin masu kai hare-hare.
Pantami ya yi wannan bayani a Abuja, inda ya kara da cewa sun shiga soshiyal midiya su kirkiri shafukan na sirri da suke watsa mugayen akidu da daukar masu kai hare-hare.
Daga nan ya ce maganin wannan sabon salon tsara kai hare-hare da ‘yan ta’adda ke yi, kawai shi ne bullo musu ta bayan-gida da dabarun fasahar hana su shiga soshiyal midiya su rika aikata barnar da suke aikatawa.
Ya ce “kirkiro sabbin dabarun fasaha kamar manhajar ‘Big Data Analysis’, ‘Internet of Things (IoT), Mutum-mutumi (Robotics) mai sarrafa kan sa da sauran na’urorin ayyukan leken asiri da na bincike za su taimaka sosai wajen kawar da ayyukan ta’addanci.”
Pantami ya ce jami’an sojoji da na leken asiri za su iya amfani da manhajar ‘Big Data’ domin su yaki ‘yan ta’adda.
Da ya ke ci gaba da yin kira ha jami’an tsaro su rungumi dabarun fasahar zamani wajen yaki da ta’addanci, ya ce saukin samar d intanet har a kayan gida kamar firinji da injin wanki a cikin gida, ya bada damar makala musu na’urorin tattara bayanai da binciken sirri wajen inganta tsaro ko zakulo masu aikata miyagun laifuka da ke boye.
Pantami ya bada misalin yadda Cibiyar Bincike ta Fasahar Zamani a kasar Qatar ta yi amfani da manhajar babban rumbun tattara bayanai na ‘Big Data’ a Facebook da shafukan twitter har ta gano wasu ‘yan Kungiyar Ta’addancin ISIS.