‘Yan sanda sun ceto mutane hudu daga masu garkuwa da mutane a Abuja

0

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa ta ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su a maboyar masu garkuwa a Abuja.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan Abuja, Anjuguri Manzah ya sanar da haka ranar Litini a wata takarda da ya raba wa manema labarai.

Manzah yace sun gano maboyar wadannan mahara ne a tsaunukan Sauni dake tsakanin Abuja da jihar Neja yayin da dakarun ‘yan sandan ke farautar su a wadannan tsaunuka.

Manzah yace masu garkuwan sun gudu sun bar mutanen dake tsare a hannun su bayan arangama da suka yi tsakanin su.

Ya ce sun yi nasaran ceto Umaru Salihu da Maryam Umaru da aka yi garukwa da su ranar 8 ga watan Faburairu sannan da Zilkifilu Usman da Usman Shuaibu wanda aka yi garkuwa da su ranar 2 ga watan Faburairu.

Manzah ya yaba goyan bayan da jami’an tsaron jihar Neja suka basu a wajen wannan aiki.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata, Rundunar ‘Yan Sandan Kasa ta bayyana kama wasu maharan kungiyar ‘Ansaru su uku da ta ke zargi su na da hannu dumu-dumu wajen kai harin yunkurin yin garkuwa da Mai Potiskum, Umar Bubaram.

Kakakin ‘Yan Sanda na Kasa, Frank Mba, ya ce an damke Munkailu Liman Isah, mai shekaru 31, Abdullahi Saminu da aka fi sani da Danmunafiki mai shekaru 21 da kuma Aminu Usman shi ma mai shekaru 21.

Ya ce an kama su sakamakon wasu bayanai na sirri bayan da ‘yan sanda suka yi wa ‘yan kungiyar Ansaru kakkabar-‘ya’yan-kadanya a Dajin Kuduru da ke Birnin Gwari, Jihar Kaduna.

Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta ce ta na tsare da mutane 8 kenan masu hannu a harin da aka kai wa Sarkin Potiskum da dare, a kan hanyar sa ta zuwa Zaria daga Kaduna, cikin watan Janairu.

Share.

game da Author