‘Yan sanda sun cafke gogarman masu garkuwa da mutane a Kaduna

0

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya bayyana cewa jami’an su sun cafke gogarman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna.

‘Yan sanda sun yi farautar mahara a dazukan Karamar hukumar Kajuru bayan sun samu rahoton sace wata mata mai suna Hadiza Gambo.

” Jami’an mu sun fantsama wannan daji bayan sun yi binciken sirri. An kama gogarman mai shekaru 57 mai suna Abubakar Gambo.

Bayan an kama Abubakar, hakan ya sa ‘yan sanda sun kai gs kama wasu abokan aikin sa biyu, Kamal Babawuro da Yahaya Gaiya a maboyan su.

Wadannan masu garkuwa sun tabbatar wa ‘yan sanda cewa suna suka karbi kudin fansa har naira miliyan 1.7 kan wani da suka sace a Kajuru.

A ceto Hadiza cikin koshin lafiya, ba tare da an biya kudin fansa ba.

Share.

game da Author