‘Yan sanda da Ali Kwara sun gano bindigogi 43 da mahara suka binne a dajin Bauchi

0

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa fitaccen mai kama barayi Ali Kwara tare da hadin guiwar ‘yansandan jihar sun jido wasu bindigogi har 43 da harsasai sama da dubu da aka binne a dajin Lame/Burra dake karamar hukumar Ningi.

Gwamna Bala ya bayyanawa manema labarai a fadar gwamnati cewa an samu nasarar kamo wadannan makamai ne a dalilin hadin guiwar jami’an yan sandan jihar da fitaccen maikama barayi Ali Kwara.

“Muna da mutane a ciki da wajen jihar nan da suke bada bayanan sirri ga jami’an tsaro game da ayyukan ‘yan ta’adda.

” Ya ce gwamnati za ata ci gaba da maida hankali wajen samar da tsaro a afadin jihar sannan kuma da kara wa shirin kafa kungiyoyin sakai karfin da kafa wasu domin kawo karshen ta’addancina a jihar.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatoci da jami’an tsaro da su hada kai da Ali Kwara domin cafko wadannan bata gario a duk inda suke.

Da ya ke bayani game da yadd suka gano inda mahara suka boye makaman da suka kwato, Ali kwara ya ce wani yaro ne suka rika bin sawu da shi har zuwa wannan daji inda suka gano wurin da aka boye makaman suka kwaso su.

” Sannan kuma akwai wani gogarman masu garkuwa da mutane da yayi kaurin suna a jihohin Taraba, Filato da Benuwai, wanda dan asalin jihar zamfara ne da muka biyo nema har wannan yanki, kafin muka cimma wannan aiki na jiran mu.

Share.

game da Author