‘Yan Majalisa sun zargi gwamnatin Buhari da yi wa majalisa da bangaren shari’a kwange da rufa-rufa

0

Mambobin Majalisar Tarayya sun sun koka da abin da suka kira kwange da rufa-rufar da gwamnatin tarayya ke wa majalisa da kuma bangaren shari’a.

Daga nan sai suka bayyana cewa za su gaggauta kafa kwamitin da zai tabbatar da ya bi kadin duk wasu kudaden ariyas din su da ba a ba su tsakanin 2018 da 2019, an biya su kamar yadda ka’ida ta nuna.

Wadannan kudaden dai daga cikin kasafin 2018 da na 2019 ya kamata a ce an biya su, kamar yadda majalisa ta yi ikirari.

Daga nan sai suka nemi sanin wane dalili zai sa Ministar Harkokin Kudade za ta rike kudaden da ya kamata a biya majalisa, amma a ki biya tsawon shekaru biyu.

Sun kuma amince za su gayyato shugabannin ma’aikatan Majalisar Tarayya domin su yi musu bayani dalla-dallla a kana bin da aka bai wa Majalisar Tarayya da wadanda ba a bayar ba, tun daga watan Janairu, 2018 zuwa Disamba, 2019.

Honorabul Babangida Ibrahim daga jihar Katsina ne ya bijiro da wannan korafin, kuma ya ce wannan magana an faro ta ne tun kafin kafa sabuwar majalisa a Mayu, 2019.

Ya ce wani rahoto ya nuna cewa “a duk wata ana bai wa Majalisar Tarayya wasu naira bilyan 1.2, bangaren shari’a kuma naira milyan 833, tun daga watan Janairu zuwa Nuwamba, 2018.

Babangida ya ce amma ba a bayar da kudaden, kuma an ki ci gaba da bayar da kudaden.

Daga nan suka ce wannan ba abu ba ne mai dorewa, za su kafa kwamitin neman bin ba’asai.

Share.

game da Author