Yadda na yi wa Kwankwaso ritaya a siyasa cikin ruwan sanyi – Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi kurin cewa yanzu fa ya yi tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ritaya a siyasa kwata-kwata.

” Idan ban manta ba lokacin da Kwankwaso ya fito takarar shugaban kasa, ya rika fadi cewa zai yi wa Buhari ritaya a siyasa har ni ma zai tabbata ban yi nasara ba. yanzu wa ye aka yi wa ritaya a siyasa?

Ganduje ya rika zaro wadannan zantuka ne a lokacin da wasu zababbun ‘yan majalisa suka ziyarce shi a fadar gwamnati.

Ganduje ya kara da cewa kaf jihar Kano kowa ya dawo daga rakiyar Kwankwaso saboda haka dama dai karshen alewa kasa.

Daga nan sai ya taya murnar yi wa mahaifin Kwankwaso, Musa Kwankwaso nadin sarautar Makaman Karaye da akayi daga majidadi.

Ya ce gwamnatin jihar na taya mahaifin Kwankwaso murnar sannan gwamnati za ta ci gaba da mara wa masarautun jihar baya domin ci gaba jihar gabadaya.

” Sannan kuma ina son in shaida muku cewa ba mu ji dadin fadowa da jam’iyyar APC ta yi a mazabar Bebeji/Kiru. Mungano cewa dan takaran ne ke da matsala da jam’iyyar a jiha, ba jihar ba kawai har da kananan hukumomin da ya ke wakilta. Wannan dalili ne ya sa mutane suka kaurace masa suka zabi PDP.

A karshe kuma, shugaban majalisar dokokin jihar Kano Garba Gafasa ya bayyana cewa majalisar za ta ci gaba da mara wa gwamnatin jihar baya do min yin nasara a ayyukan ci gaba da ta sa a gaba.

Share.

game da Author