Kwanaki biyu bayan da mahara suka yi wa garuruwan Dankar da Tsanwa dirar mikiya a jihar Katsina, har suka kashe mutane 31, an kuma tabbatar da cewa Boko Haram sun kai hari a garin Babbangida, hedikwatar Karamar Hukumar Tarmuwa, cikin Jihar Yobe.
A yayin harin, Boko Haram sun kuma banka wuta a kan karfen turken na’o’urar waya na MTN a garin.
Sun kai wannan hari ne da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda Premium Times ta samu tabbacin kai harin daga bakin Kakakin Yada Lanarai na sojoji.
Ya ce abin da Boko Haram su ka yi niyyar yi shi ne daga Babbangida su zarce su shiga Damaturu, amma ba su samu dama ba, saboda sun gamu da gamon su a hannun sojojin Najeriya.
Har yanzu dai ba a bayyaa wadanda aka kashe ko aka jikkata a wannan gumurzu da sojoji ko harin ko harin da Boko Haram suka kai a Babbangida ba.
Wani babban jami’in sojoji ya shaida wa Premium Times cewa Boko Haram sun kutsa cikin Babbangida tare da motocin daukar bindigogin harbo jirage su biyar da kuma wasu biyu da suka girke a bayan garin na Babbanjida.
Mazauna garin sun ce maharan sun banka wa turke na’u’rorin layin MTN wuta.
Premium Times ta yi kokarin jin ta bakin wasu ‘yan cikin garin a lokacin da aka kai musu harin, amma an kasa samun su.
Wannan kuwa alama ce mai nuna cewa an lalata turke wayar MTN kenan a garin.
Kakakin Yada Labarai na Sector 2, Operation Lafiya Dole, Damaturu, Chinonso Oteh, ya tabbatar da an kai wannan hari.
Ya ce Boko Haram sun yi kokarin shiga Damaturu ne, “amma sun samu cikas, bayan da sojojin mu da zaratan mayaka na sojojin sama da su ma suka kai dauki da hanzari.’
“Gaskiya Babbangida dandali ne Boko Haram kan rika fada yada zango sau da dama kafin su shiga Damaturu.”
Amma dai yanzu babu wata barazana, komai ya daidaita, kamar yadda ya yi bayani.
Babbangida ta na da tazarar kilomita 50 daga Damaturu.