TSARO: Masu garkuwa sun kashe mutum biyu cikin kwana daya

0

Ikirarin da Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta yi cewa gwamnatin ta fi gwamnatocin baya yaki da rashin tsaro a kasar nan, ya haifar da ka-ce-na-ce, yayin da masu garkuwa da mutane suka kashe mutane biyu a ranar Asabar da ta gabata, a cikin Jihar Kaduna.

Mutane biyun da aka kashe dai akwai wani matashi mai shekaru 18, mai suna Micheal Nnadi da kuma matar wani likita mai suna Philip Ataga, wani mazaunin Kaduna.

An tsinci gawarwakin su biyun a gefen titi, ranar Asabar din nan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama Nnadi an yi garkuwa da shi tun ranar 8 Ga Janairu, ita kuma Ataga an kama ne a ranar 24 Ga Janairu, cikin Karamar Hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Kafin masu garkuwa su kai ga kashe Ataga, sai da suka nemi a ba su kudin fansar ta har naira milyan 150 domin su sake ta tare da ‘ya’yan ta biyu da suka yi garkuwa da su.

Masu garkuwa da mutane sun kashe Ataga, suka jefar da gawar ta, sannan suka kira mijin ta tare da sanar da shi inda zai je ya dauki gawar matar ta sa.” Haka aka ruwaito.

Amma kuma har yanzu da ake rubuta wannan labari, masu garkuwa da mutanen sun ce ba za su saki ’ya’yan ta biyu ba, har sai an biya fansar naira milyan 20.

An yi garkuwa mai wa coci hidima Nnadi tare da wasu masu yi wa coci hidima wasu uku, Pius Kanwai, Peter Umenukor da Stephen Amos, a Cocin ‘Good Shepherd Major Seminary’, Kaduna.

Masu garkuwa sun saki sauran mutanen uku a ranar Juma’a, shi kuwa Nnadi sai gawar sa aka tsinta washegari ranar Asabar.

Share.

game da Author