Sojoji sun yi gumurzun hana Boko Haram sake shiga Maiduguri

0

Ranar Lahadi wajen 7:30 na dare ne sojoji da ke tsaron wani shinge tsaro kusa da kauyen Ngwom, suka yi gumurzun hana wasu gungun Boko Haram sake shiga Maiduguri.

Boko Haram sun kai wa garin hari a ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje da ta’aziyyar matafiya 30 da Boko Haram suka kashe tare da banka wa motocin matafiya wuta a garin Auno, kusa da Maiduguri.

Shi kuma wannan yunkuri na baya-bayan nan da Boko Haram suka sake yi, sun yi shi ne kusan daidai lokacin da Boko Haram suka afka garin Babbangida da harbe-harbe, a Karamar Hukumar Tarmuwa, cikin Jihar Yobe.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin harin Babbangida, inda ta bayyana mahara sun kai hari har da lalata turakun wayar layukan MTN da ke garin.

A yunkurin sake shiga Maiduguri, an rika jin harbe-harbe da tashin bindigu wajen 7:30 na dare har kusan awa daya babu kakkautawa.

Karar ta rika fitowa ne daga wajen Muna, mashigar Maiduguri a kan hanyar Gamboru-Ngala, inda mazauna yankin suka kasance cike da fargaba.

Wani mai suna Ahmadu Haga da ke aiki a sansanin masu gudun hijira da ke Muna, wanda dan sintiri ne, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa lallai an yi wannan gumurzu tsakanin sojoji da Boko Haram.

“An kai harin ne a wani wuri kusa da Kaliyari, can bayan inda unguwar mu ta ke.”

Shi kuwa wani jami’in CJTF na jami’an tsaron hadin guiwa, ya shaida wa wakilin mu ta wayar tarho cewa “an kai wa shingen tsaron sojoji harin ne, amma su ma suka fatattake su a shingen kusa da kauyen Ngwom.

“Sun yi kokarin shigowa cikin Maiduguri, sai suka fara kai hari a shingen sojoji. Amma cikin ikon Allah sojojin sun tsaya tsayin-daka sun fatattake su.”

Amma Danbatta bai ce ga yawan wadanda aka kashe ko wadanda suka jikkata ba.

Share.

game da Author