Sojojin da aka girke a Moriki cikin Jihar Zamfara, sun bada sanarwar yin arba da wani dauke da buhun da aka tsatstsage da tulin harsasai.
Sun ce an yi arba da mai babur din ne dauke da buhun a ranar Litinin, wanda ya nuna kamar buhun shinkafa ne ya ke dauke.
An ce mutumin da ke tuka babur din ya arce ya bar babur da buhun albarusai din, kamar yadda aka tabbatar.
An samu albarusai 4653 a cikin buhun, wanda buhun zuba shinkafa ne.
Majiya a cikin sojoji ta shaida cewa sun samu tsegumin wani zai yi jigilar albarusai a ranar Litinin a yankin Moriki. Wannan ne ya sa su ka kafa shingen bincike.
“Ba a dade da kafa shingen bincike ba, sai ga wani dauke da buhu a bayan babu. Kai ka ce shinkafa ce ya dauko.
“An tsaida shi, amma ya ki tsayawa. An bi shi amma ya tsallake ya bar babur da buhu, ya tsare.
Majiyar ta ce bayan an bincika sai aka samu harsasai girmis a cikin buhun da a baya aka yi tsammani buhun shinkafa ne.
Baya ga hare-haren masu garkuwa da kashe mutane a Zamfara, talauci da fatara sun yi wa jihar katutu, akwai yaran da ke gararamba a gari ba su zuwa makaranta kimanin su 422, 214, kamar yadda hukumar kula da ilmin bai firamare, wato UBEC ta fitar da kididdiga.
Discussion about this post