Wani soja mai mukamin Kofur, ya dirka wa wani Dan Sandan Mobal bindigar igwa da ake harbo jirage da ita.
Wannan tsautsayi ya faru a Makara cikin Karamar Hukumar Gwoza, Jihar Barno. Majiya ta bayyana cewa an dirka wa Sajan Ronald Tafida harbi da igwa, saboda hatsaniyar da ta faru tsakanin sojan da wani dan sanda can daban.
An tura Ronald Tafida aikin Musamman Kan Dakile Ta’addanci na tsawon watanni shida, kuma har ya kammala ya na shirin barin Gwoza a ranar Asabar, 8 Ga Fabrairu, sai aka bindige.
Majiya ta ce lamarin ya faru ne sanadiyyar cacar-baki a kan wata budurwa da majiya ta ce an yi tsakanin Kofur din soja da wani dan sanda.
Wata majiya ta ce ba da Rowland aka yi hatsaniyar ba, shi tsautsayi ne kawai ya fada a kan sa.
“Sojan da shi da dan sandan sun yi tankiya mai zafi, amma aka shiga tsakanin su. Ashe Sojan nan bai hakura ba.
” Sai ya umarci direban mota kirar Hilux da ya ke ciki mai dauke da bindigar igwa ta harbo jirage, ya ce su yafi ofishin ‘yan sanda na Liman Kara.
“Su na isa sai hasalallen sojan nan ya hau bisa mota ya yi saitin ofishin ‘yan sanda, ya dankara harbi.
Harsashe ya samu Rowland Tafida a lokacin da ya ke komawa daga inda ya kai cajin wayar sa.
Harbi ya ragargaza cinyar Tafida, ya fadi jini na zuba, kuma aka rasa wanda zai dauke shi zuwa Asibiti.
An bar shi a wurin kwance har ya mutu, sai daga bisani ‘yan sandan mobal suka fito suna zanga-zangar rashin amincewa.
Ba don wani babban soja ya shiga tsakani ba, da abin ya baci. Daga bisani an dauki gawar dan sandan zuwa asibitin spjoji a Maiduguri.
Rundunonin jami’an tsaron biyu sun kafa kwamitin binciken gano musabbabin kisan, bayan an kama sojan da ya yi harbin.