SIYASAR HANA BARA: Su wane ne Matsalar Arewa?

0

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya yi kaifin tunani da ya ce, “idan ma har ta kama sai mutum ya yi bara, to gwamnati ya kamata ya yi wa bara, ba jama’ar gari ba.” A nan ni ma na yarda da shi. Wannan magana da ya yi, abin dubawa ce, kuma a kan ta wannan sharhi zai yi warwarar zare da abawar matsalar barace-baracen da ake fama a Arewa.

Babban abin mamaki a Arewa shi ne yadda shugabannin siyasa ke ta fadi-tashin maganganu dangane da batun matsaloli da illolin barace-barace. Karin abin mamaki kuma shi ne yadda ’yan siyasar ke nuna kamar barace-barace ne kadai matsalar Arewa.

Su Wane Ne Matsalar Arewa?

A ganin wasu da an kawar da almajirai, ko kuma dai kai-tsaye na ce mabarata a kan titi, to shikenan matsalolin Arewa sun gushe. Wannan kuma karya ce!

Masu rike da shugabanci, tun daga Karamar Hukuma, Jihohi da suka hada da Majalisun Jiha, Kwamishinoni, masu rike da mukaman ayyukan gwamnati, gwamnoni, ministoci har zuwa shugabannin kasa da duk wani mai rike da babban mukami dan Arewa, su ne suka kara assasa yawaitar mabarata a Arewacin kasar nan. Kuma matsalar Arewa daga cikin da yawan su ta samo asali.

Duk wani wanda ya rike babban mukami a Arewa, makarantar gwamnati ya yi firamare da sakandare. Amma a yau duk sun kwashe ’ya’yan su daga cikin ’ya’yan talakawa a makarantun gwamnati.

Yawancin makarantun gwamnati ba a koyar da abin kirki, babu malaman kirki, kuma ba a cin jarabawar kirki. Sannan kuma ba a samun ’ya’yan talakawa masu tafiya makarantun kirki irin wadanda ‘ya’yan masu rike da mukamai ke kai ‘ya’yan su. Don me kuwa ba za a samu marabata ba? Shin talakawa ke sace kudaden inganta ilmi ko kuwa manyan jami’an gwamnati?

Yaya kuwa ba za a samu mabarata a Arewa ba, tunda jami’an gwamnati na satar kudin harkokin noma, talaka ba ya iya samun takin zamani. Ba ya iya noma wadataccen abinci. An saci kudin noma jami’in gwamnati ya zama biloniya. An saci kudin kiwon lafiya, jami’in gwamnati ya zama biloniya. An saci kudin harkar tsaro, jami’in gwamnati ya zama biloniya. An sace kudaden inganta karkara, jami’in gwamnati ya zama biloniya.

An bar talakawa a cikin kunci, talauci da fatara, sannan kuma a ce fakiri ba zai yi bara ba. Su a ganin su duk wadannan masu sace kudaden ba su ne matsalar Arewa ba, sai mai neman ku ba shi abin da ku ka ci ku ka rage, ku da ‘ya’yan ku. Wai shi ne matsala, alhali kuma ku ne ku ka haifar masa da matsalar.

Daga shekara 10 zuwa yau mabarata sai karuwa su ke ta yi a Arewa. Ko kuma na ce sai nunkawa su ke yi. Don me kuwa mabarata ba za su nunka ba, tunda an ware kudin sayen makamai, amma manyan Arewa sun danne kudaden, sun bar Boko Haram na tarwatsa kauyuka, an kashe uban yaro, an tsere da mahaifiyar sa, an kone gidan sa. Kai kuma ka saci kudin sayen makamai, kuma wai ba ka son wannan yaron ya yi bara. Karya ka ke yi!

Har yau a Arewa yankunan da babu ruwan famfo sun fi masu famfon yawa. Ina kudaden ayyukan ruwan da ake warewa a kasafin kudi na jiha da tarayya da tallafin da hukumomi da kungiyoyin kasashen waje ke aikowa? Ko su ma mabaratan ne suka sace kudaden?

Kwata-kwata babu kyakkyawan tsarin kiwon lafiya a Arewa. Yau idan matsalar naira 40,000 ta same ka, sai dai ka mutu, amma babu asibitin gwamnatin da za a iya raba ka da ciwon kyauta. Sai fa abokan arziki sun mena maka gudummawa a soshiyal midiya.

An wayi gari a Arewa duk ciwo da ya kama talaka, to Allah ne gatan sa, sai kuma wasu kungiyoyin mata masu gaganiyar neman gudummawar taimakawa daga hannun jama’a, ba daga hannun gwamnati ba ko asibitin gwamnati.

Amma kuma a jihar ka, yau sai ka ji an kama wane ya karkatar da naira bilyan daya, gobe wani ci biyan biyu. Kuma wai duk wadannan su ba matsala ba ne, sai wanda ya fita neman barar neman kudin maganin asibiti, shi ne matsala a Arewa. Karya ku ke yi! Sai mabarata sun dame ku da bara.

An haife ka a karkara, ka tashi a karkara, ka yi makarantar gwamnati kyauta. Amma da an ba ka mukami babu abin da za ka fara sai sace kudin gwamnati wadanda za a yi wa mutanen karkara aiki. Kai kuma a karshe ka gina gidaje ko ka sayi makamakan jigaje da kudin da ka sata a Abuja.

Kai ba ka amfana ba, talakawa ba su amfana ba, kuma wai kai a ganin ka, ba kai ne matsalar Arewa ba, sai mabaraci. Karya ka ke yi.

Wani matsiyacin ma idan ya kwashe kudaden waje zai je ya boye, har ya mutu ba za a san inda ya boye kudin ba. Ga kauyen su ko kwalta babu. Amma ba son ganin mabaraci a cikin birane. Karya ka ke yi!

Don me kuwa dan Arewa ba zai yi bara ba, musamman a cikin shekarun nan 10 zuwa yau? An je har gida an kwashe maka shanu 50, an banka wa kauyen ku ko rugar ku wuta. Ga sawun da aka shiga jeji da shanun, amma an kasa kwato maka hakkin ka. Ka wayi gari ko abincin yau da na gobe babu a gidan ka. Kuma idan kai ko dan ka ya shigo gari ya yi bara, to kai ne matsalar Arewa ba manyan barayin Arewa ba. Karya ku ke yi!

A zaman yanzu haka akwai masu gudun hijira daga Najeriya a cikin Nijar sun kai mutum 120, 000, idan ma bas u fi ba. Allah kadai ya san yawan wadanda ke nan cikin Najeriya. Wadanda ‘yan bindiga suka fatattaka daga kauyuka, sun shigo gari su na neman cin abin da aka ci aka rage, wai kuma su ne matsalar Arewa, ba wadanda suka yi rantsuwar kare lafiya, dukiya da rayukan su ba.

Yau da a ce manyan Arewa su na tausayin halin da Arewa ke ciki, su na maida hankali kan raya Arewa kamar yadda Bill Gates ke tsallakowa daga Amurka ya na tallafa mana a bangaren lafiya da sauran su, to matsalar Arewa ta barace-barace da ta ragu matuka.

Amma wace burga wani dan siyasa zai yi wa Arewa, bayan ya kwashe kudin raya karkarar Arewa, kunci da talauci da fatara da Boko Haram da ‘yan bindiga sun koro jama’ar karkara su na barace-barace, sannan kuma wai mai bara shi ne matsalar Arewa. Karya ku ke yi!

Yanzu idan kuri’ar-raba-gardama za a yi, a ce tsakanin manyan ’yan sisayar Arewa da masu rike ko wadanda suka rike mukaman gwamnati ’yan Arewa, da kuma mabaratan Arewa, shin su wa suka kashe Arewa? Na tabbata mutum ko a buge ya ke ba zai ce mabarata ba ne.

Ina mamakin masu cewa mabarata na zubar wa Arewa mutunci, alhali kuma ga mu tare da garsaka-garkasan wadanda suka takaita Arewa, suka tsiyata yankin ta hanyar kwashe kudaden da suka kamata a raya al’umma da su.

Ba za a yi jam’u ba, na san akwai da yawa wadanda suka yi ayyukan raya kasa, suka inganta jihohin su, kuma suka kafa tarihin da kowa ya sani. Mun kuma san su. Su ma sun san kan su.

Arewa babu jihar da ke iya ciyar da kan ta. Tilas a duk wata sai an jira kudaden fetur daga hannun gwamnatin tarayya. Amma kuma wadannan kudaden su ne dai ake ci gaba da yi wa rub-da-ciki kan wadanda za a iya dannewa.

Da yawa tilas ce ke sa su bara. Da yawa tilas ce ke sa ’ya’yan su bara. Da dama kuma rashin ingancin ilmin firamare ne ke sa su tura
‘ya’yan su makarantar allo. Saboda ko yaron ka ya shekara 20 a firamare ko sakandare, ba cin jarabawa zai yi ba. Saboda babu ilmi mai inganci.

Su kan su malaman da kwamishinan ilmi da kowa bai yarda da ingancin ilmin makarantar gwamnati ba. Shi ya sa ba mai kai dan sa makarantar gwamnati. Ka ga kuwa, da yaro ya yi biyu babu, sai mahaifin sa ya ga har gara ma ya tura shi makarantar allo. Shi dama mahaifin yaro zaman wahala ya ke yi a karkara, wa ruwa, ba wuta, babu asibiti, babu tallafi, babu taki. Amma kuma a duk wata ana karbo bilyoyin nairori daga gwamnatin tarayya.

Ina Mafita?

Na tabbata ba za a iya kawar da mabarata a Arewa ba, har sai shugabannin mu sun canja tukunna. Idan za a gyara, to a gyara da wuri. Amma dai laifin lalacewar Arewa da yawan mabaratan ta, ba na mabaratan ba ne.

Kun danne kudaden al’umma, kun boye a waje da sauran wurare. Kun kamfaci kudaden al’umma kun gina manayan gidajen da babu masu kwana a ciki. Kun kwashi kudade kun sayi manyan motocin alfarma kun shige.

Boko Haram da ’yan bindiga sun ragargaza karkakar yankunan Arewa. Jama’a sun bazu, sun gudu cikin karkara, sannan kuma ku ce don me ba za su yi muku bara a bakin danja ko cikin tasha ko kan titi ba. Karya ku ke yi!

Ba za a daina yi muku barace-barace a Gadar Kawo, kasuwannin Kano da kan titinan garuruwan Arewa ba, har sai ’yan-yaga riga sun daina kekketa rigar mutuncin Arewa, mun dawo taitayin mu tukunna.

Share.

game da Author