Siffofi Da Akidun ‘Yan Ta’adda Da Hadarin Yaduwar Su A Cikin Al’ummah! Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.

Ya ku ‘yan uwa na masu girma, da ikon Allah, a wannan karon, cikin wannan sako nawa ina so ne in yi muna bayani takaitacce game siffofi da hadarin akidar ‘yan ta’adda da sharrin da ke tattare da wadannan kungiyoyi a cikin al’ummah.

Ya ku jama’ah, lallai kamar yadda kowa ya sani ne, Allah Subhanahu wa Ta’ala ya jarabi wannan kasa ta mu wato Najeriya, da kuma wasu sauran kasashen afirka, kamar Nijar, Kamaru, Mali, Chadi da sauran su, kai da ma yankin da ake kira yankin Sahel, da ma duniya baki daya, da wadannan kungiyoyi na ‘yan ta’adda, kungiyoyin sharri, kungiyoyin fitina; wadanda basu komai illa yada barna, sharri, ta’addanci, kisa da zubar da jinin bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba.

Wadannan ‘yan ta’adda sun addabi al’ummah, sun zama alakakai, suna bata sunan Musulunci da Musulmai, musamman a wurin wadanda ba su fahimci addinin ba!

A nan Najeriya, Allah ya jarabe mu da kungiyoyin ta’addanci, wadanda suka dauki makamai domin su yaki gwamnati da al’ummah baki daya, irin su: Jama’atu Ahlis-Sunnah lid-Da’awati wal Jihad, wadda aka fi sani da suna Boko Haram, da Ansaru, da ire-iren su. Sannan bayan su akwai wadanda basu kai ga daukar makamai su yaki hukuma ba, su kawai suna amfani ne da harsunan su a wurin wa’azi, da kan mimbarorin huduba, suna caccakar gwamnati, suna yin batanci ga shugabanni, suna zuga al’ummah domin su juya wa shugabannin su baya. Wanda irin wadannan kungiyoyi, In Shaa Allahu su ma zan samu lokaci domin yin bayani akan su, ba domin komai ba sai domin al’ummah ta san su, ta guje su, kuma domin hukumomi su san cewa lallai idan za’a dauki mataki, to dole ne a hada har da su, matukar ana so a kawo karshen ta’addanci da ‘yan ta’adda a Najeriya, da ma duniya baki daya.

Ya ku jama’a, lallai ku sani, zan ambato muna siffofin wadannan ‘yan ta’adda, domin mu san su, mu guje su, kuma mu san ta inda ya kamata mu bullo masu.

Ya zama wajibi hukuma ta dauki matakin da ya dace a kan su. Ya zama dole iyaye da dukkanin masu ruwa da tsaki wurin tarbiyyar ‘ya’ya da tarbiyyar matasa su san da wadannan siffofi, domin mu hana ‘ya ‘yan mu da matasan mu shiga wadannan kungiyoyi na sharri.

Yanzu haka da nike wannan rubutu, wallahi ba mu san iyakar matasan mu da suke ruduwa da kamfen din wadannan ‘yan ta’addar ba, har suke shiga cikin kungiyoyin su, suna addabar al’ummah. Wallahi, wallahi, wallahi ina shaida maku da Allah cewa, na san matasan mu da dama da suka tafi garin Maiduguri, suka tafi kasar Syria, Libya, Afghanistan, Somalia da sauran kasashe da dama, suka shiga wadannan kungiyoyi na ‘yan ta’adda, da sunan za su yi jihadin Musulunci, alhali duk wani mai hankali da ya fahimci shari’ar Musulunci, yasan cewa wadannan mutane fasadi suke yi ba jihadi ba. Saboda haka wallahi ya zama dole ga hukumomi da al’ummah baki daya, mu hada kai, mu tashi tsaye, mu shiga taitayin mu, domin akwai jan aiki sosai a gaban mu.

A mataki na duniya da ma nan gida Najeriya, muna da kungiyoyin ta’addanci kamar: Taliban, Boko Haram, Ansaru, Al-Shabab, Al-Qa’idah, ISIS, ISIL, ISWAF da sauran su.

Sannan ga kadan daga cikin siffofi da akidun wadannan kungiyoyi na ‘yan ta’adda domin mu san su, mu san yadda zamu yake su, yadda zamu guje su, yadda zamu hana matasan mu shiga cikin su, da yadda kuma zamu hana yaduwar su a cikin al’ummah, da yadda zamu yaki duk wasu masu irin wadannan munanan akidoji, domin hadarin su a tsakankanin mu yana da yawa. Daga cikin siffofin su:

1. Suna kafirta duk wanda ba ya tare da su a cikin akidar su, cikin batan su da barnar su, kuma suna halatta jinin sa. Don haka zaka ga cewa za su iya halaka ko wanne mutum matukar ba ya tare da su, kuma komai matsayin sa, kuma komai rikon sa da addini, matukar ba irin addinin su na ta’addanci yake yi ba.

2. Sun kira sauran Musulmai da cewa duk sunyi ridda, sun kafirta, sun fita daga addinin Musulunci, don haka wajibi ne a yake su. Suna ganin cewa dukkanin garuruwan Musulmai a halin yanzu sun kafirta, garuruwa ne na kafirai, don haka yakar su wajibi ne domin a dawo da su akan tafarkin Musulunci, kuma ayi jihadi a kafa daular Musulunci. Alhali duk muna sane cewa, Annabi (SAW) ya hana a kafirta Musulmi.

3. A irin ta su murdaddiyar fahimtar addinin Musulunci, suna ganin cewa duk wasu shugabannin siyasa, da sarakuna, da alkalai, da dukkanin nau’ukan jami’an tsaro Musulmai, da ‘yan boko Musulmai da ma’aikatan gwamnati Musulmai, duk sunyi ridda, don haka kafirai ne, hukuncin su shine a yake su, a kashe su, domin a huta da barnar su.

4. Suna kallon duk wata gwamnati da bata kan tsarin addinin Musulunci kafira ce, dole ne a yake ta tare da dukkanin ma’aikatan ta da jami’an ta. Domin suna cewa ita dagutu ce kuma ma’aikatan ta suna goyon bayan dagutu.

5. A wurin wadannan jahilan ‘yan ta’addan, ba tare da rarrabewa ba, sunan ganin duk wani shugaba wanda bai yi hukunci da alkur’ani ba to shi kafiri ne, don haka wajibi ne a yake shi, a kifar da gwamnatin sa, a kafa daular Musulunci.

6. Sannan su a wurin su, ya halatta su aikata komai, kuma ko da haram ne, ko da laifi ne, ko da barna ne, matukar zai kai su ga cimma nasara akan aikin su na ta’addanci (الغاية تبرر الوسيلة عند هم meaning: For them the end justify the means).

7. Wallahi na san ‘yan ta’adda da dama wadanda suke shaye-shaye; suna shan ko wane irin nau’i na kayan maye; suna shan kwayoyi, tabar wiwi, taba sigari a filin Allah, ba kunya ba tsoron Allah, amma daga baya sai ka ga suna kafirta iyayen su da sauran Musulmai. Don haka, dan ta’adda ya halaka iyayen sa ma ba wani abu ba ne a wurin sa, domin yana ganin idan ya kashe su to yayi abu mai kyau, yayi jihadi, yayi aikin Allah. Don Allah mu tafi jihar Borno, muyi bincike mu gani, wallahi za ka tarar da iyaye da dama, wadanda ‘ya ‘yan su ne da suka haifa da cikin su, suka yi masu yankan rago!

8. Daga cikin siffofin ‘yan ta’addan yau shine, yawan sa bakaken tufafi, kamar ‘yan shi’a ko kiristoci. Alhali mun san cewa sanya fararen tufafi shine Sunnar Annabi (SAW). Babu inda aka samu cewa Annabi (SAW) ya lizimci sanya bakaken kaya a rayuwar sa. Amma su ‘yan ta’adda sun bar wannan Sunnah, kullun za ka gan su a cikin bakaken tufafi. Sannan suna barin gashin kan su ya taru, yayi yawa, sabanin khawarijawan da, wadanda su suna aske gashin kan su ne kwal-kwal.

9. Kamar yadda Annabi (SAW) ya bamu labari daga cikin siffofin su shine, suna kashe Musulmai amma suna barin kafirai, arna masu bautar gumaka. Ma’ana, ‘yan ta’adda sun fi jin haushin Musulmai akan kafirai, saboda su a wurin su, duk Musulmin da basu ba to riddade ne! Shi yasa zaka tarar cewa ‘yan ta’adda sun fi cutar da al’ummar Musulmai da aikin su na ta’addanci!

10. Kungiyoyin ta’addanci suna ganin cewa halal ne a kai harin kunar bakin wake, halal ne a dasa bama-bamai, a rika kai harin kwanton bauna da sari-ka-noke, a kashe jami’an tsaro (sojoji, ‘yan sanda da sauran su). Kamar yadda Malaman su suka basu fatawa. Don Allah ka binciki fatawowin malaman su, irin su, Abu Muhammad Al-Maqdisi, da Abu Qatadah Al-Filistini, da Abu Yahya Al-Libi, da Abu Hamza Al-Misri, da Anwar Al-Awlaki, da Abdallah Faisal, da Umar Abdur-Rahman, da Abu Basir At-Tartusi da sauran su, wallahi zaka ga cewa sun yi fatawar halaccin kai harin kunar bakin wake, kai ko da a cikin jama’ah ne. Kuma ba su damu ba, ko waye zai mutu a wannan hari, kamar mata, yara, tsofaffi da sauran su. Kuma suna ganin cewa a fara yakar Musulman da suka yi ridda, shi yafi dacewa, kafin a yaki wadanda ba Musulmai ba.

11. ‘Yan ta’adda sun halatta kashe kiristocin da ake zaman lafiya da su. Wadanda suke da alkawarin amana a kan su tsakanin su da Musulmai, da wadanda suke karkashin jagorancin shugaba Musulmi. Sun jahilci cewa Musulunci ya halatta muna yin huldar kasuwanci da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da wadanda ba Musulmai ba.

12. ‘Yan ta’adda sun mayar da yanka Dan Adam, irin yankan rago ba bakin komai ba. Matukar dai ba ka tare da mummunar fahimtar su, ko kai Musulmi ne ko kai kirista ne to za su iya yanka ka, domin wannan ba wani abu ba ne a wurin su. A tarihin Musulunci, wallahi ba’a taba samun inda Annabi (SAW) ya yanka wani ba, ko yasa aka yanka wani. Idan kuma akwai, to ina kalubakantar ‘yan ta’adda su kawo muna a ina ne! Hadisin da suke kafa hujja da shi, wallahi sam bai tabbata daga Manzon Allah ba, kamar yadda Ibn Hajar ya nuna.

Yanka Dan Adam wallahi hanya ce tun asali ta mabarnata, halakakku, khawarijawa, ‘yan ta’adda. Tarihi ya nuna cewa, magabatan su sun taba yanka Sahabin Annabi (SAW) mai suna Abdullahi Bin Khabbab kamar yankan rago!

Don haka a addinin Musulunci ba’a yanka Dan Adam, idan ma har mutum ya aikata laifin da a Shari’a ya cacanci kisa, toh akwai hanyoyin da aka yi umurni a kashe shi, ba ta hanyar yi masa yankan rago ba!

13. Na daga siffofin su, ‘yan ta’adda jahilai ne, sam basu fahimci addinin Musulunci ba. Kuma ba sa girmama Malaman Allah, Malaman gaskiya. Shi yasa suke alfahari da kashe Malaman addini. Kuma sannan suna karatun Alkur’ani da Hadisan Annabi (SAW), amma ba su gane komai.

14. Za ka tarar da cewa mafi yawan su matasa ne a cikin tafiyar su, yara ne, samari ne (حدثاء الاسنان). Sannan kuma za ka tarar mafi yawan su wawaye ne, marasa wayo da hankali (سفهاء الاحلام). Kuma zaka tarar suna da dadin baki, sun iya bayani da zance, ta yadda za su iya jawo hankalin matasa zuwa ga shiga cikin kungiyoyin su (يقولون من خير قول البرية).

15. Annabi (SAW) yace, suna fita daga cikin addinin Musulunci kamar yadda kibiya ta ke fita daga cikin baka! Shi yasa ma wasu Malamai (kamar Sheikh Bin Baz da sauran su), suke ganin cewa ‘yan ta’adda kafirai ne ba Musulmai ba ne. Amma dai zance mafi inganci shine, su Musulmai ne amma fasikai, ‘yan ta’adda, mabarnata!

16. Akwai su da kokarin ibadah da bautar Allah, amma duk a banza, saboda ba su mayar da jinin Dan Adam a bakin komai ba!

17. Daga cikin dalilan da ke sa ‘yan ta’adda su bayyana, su addabi al’ummah, shine, rashin hadin kan Musulmai, kamar yadda Annabi (SAW) ya fada a cikin Hadisi ingantacce. Jama’ah don Allah mu kalli yadda al’ummar Annabi Muhammad (SAW) ta karkasu a yau, kungiya-kungiya, jama’ah-jama’ah, Darika-Darika, Shi’a-Shi’a! Kuma kowa kungiyar sa ko darikar sa kawai ya sani, kuma ita kawai yake yiwa aiki da hidima. Kuma ni har yanzu ba’a amsa mani tambayoyi na ba akan matsayin kafa kungiya ko darika a cikin addinin Musulunci. Nayi tambaya cewa, don Allah meye sunan kungiyar Annabi (SAW) da Sahabban sa ko kuma sunan darikar su ko sunan Shi’ar su? Sannan nayi tambaya cewa, shin akwai wanda idan ya mutu, ya hadu da Allah, Allah zai tambaye shi akan kungiyar sa ko darikar sa ko Shi’ar sa? Har yanzu wallahi babu wanda ya bani amsa gamsashshiya akan wadannan tambayoyi! Don haka wallahi ya zama wajibi muji tsoron Allah, mu riki addini irin wanda Annabi (SAW) da Sahabban sa suka yi, don mu samu zaman lafiya mai dorewa!

Shi yasa duk wadannan kungiyoyi na ta’addanci zaka tarar wallahi suna samun karfi ne a lokacin da al’ummar Musulmai suke rarrabe, suka kasa hada kawunan su akan gaskiya, domin tunkarar matsalolin da ke addabar su.

Duk irin wannan rashin hada kai akan gaskiya shine ya jawo makiyan mu suke hada kai da ‘yan ta’adda, suna rusa kasashen Musulmai, kuma ake kan rusawa. Don Allah dubi Afghanistan, Iraq, Syria, Egypt, Libya da sauran su! Makiya Musulunci suna aiki tare da irin wadannan kungiyoyin ta’addancin domin rusa kasashen Musulmai ne idan Musulmai sun kasance a warwatse, suka zama kungiyoyi daban-daban, suka rarrabu.

Don haka sai mun hada kai akan gaskiya sannan Allah ya taimake mu. Idan ba haka ba kuwa…

18. Malamai magada Annabawa ne. Amma ‘yan ta’adda sam basu girmama Malamai ko kadan. Sun dauke su ba bakin komai ba. Suna jifar Malamai da zargi iri-iri. Suna kiran su mayaudara, maha’inta, Malaman gwamnati, kai suna ma kafirta su, suna kai hari domin su kashe su, saboda Malamai suna tona masu asiri, suna bayyana wa jama’ah aibin su, barnar su, hadarin su da sharrin su. Haka magabatan su suka yi, suka kafirta Sahabban Annabi (SAW).

19. Daga cikin siffofin ‘yan ta’adda shine, suna dora ayoyi da nassoshin da aka saukar akan kafirai ga Musulmai.

20. Daga cikin siffofin su shine, su kan su ‘yan ta’adda ba yadda za’a yi su hadu. Zaka tarar da su suna kafirta juna, suna yakar juna, suna farautar juna su kashe. Ga su nan da yawa, amma basu yarda da junan su ba. Misali akwai Jama’atu Takfir wal hijrah, akwai Al-Qa’idah, akwai Jabhatun-Nusrah, akwai Jama’atu Jihad, akwai ISIS, ISIL, ISWAF, Boko Haram, Ansaru, Al-Shabab da sauran su. Misali, anan Najeriya, bangaren kungiyar dan ta’adda Shekau suna farautar juna da bangaren su dan ta’adda Mamman Nur. Sannan shugabannin ISIS suna kafirta shugaban Al-Qa’idah da jama’ar sa, wato Ayman Al-Zawahiri, kuma da zasu same shi wallahi kashe shi za su yi. To haka dai sha’anin ‘yan ta’adda yake a koda yaushe.

21. ‘Yan ta’adda suna da fahimtar cewa, kawai a dauki makamai a yaki azzaluman shugabanni. Duk da tarin Hadisai da aka ruwaito daga Annabi (SAW) cewa, muyi hakuri da su, muyi masu addu’a da fatan alkhairi, muyi masu biyayya, kar muyi masu ihu, kar muyi masu tawaye. Amma duk wata kungiya ta ‘yan ta’adda da ka sani, ba su yarda da wadannan Hadisan ba! Za ka same su suna yakar shugabanni, suna yi masu tawaye. Wallahi ko ihu da aka yiwa shugaba Muhammadu Buhari a garin Maiduguri kwanan nan sam bai dace ba, domin wannan hanya ce da koyarwar ‘yan ta’adda!

Sannan babu wani halastaccen shugaba da ‘yan ta’adda suka yarda da shi ayau. Shugabannin su kawai suka yarda da su. Suna ganin cewa duk shugabannin da muke da su ayau ya wajaba ayi masu tawaye, a tunbuke su, domin su sa nasu shugabannin da suka amince da su.

22. ‘Yan ta’adda suna fassara ayoyin Alkur’ani da dukkanin nassoshi daidai da ra’ayoyin su, fassarar da ta dace da barnar su. Duk wata fassara ta magabata, indai ba irin fassarar su bace to shirme ce, kuma ba su yarda da ita ba.

23. ‘Yan ta’adda ba su tsayawa su koyar da al’ummah addinin Musulunci. Ba su bai wa koyar da ilimi muhimmanci. Kawai abunda suke bai wa muhimmanci, kuma suke damuwa da shi, shine maganar jihadi da gwagwarmaya. Kuma jihadin ma sun ki su tsaya su fahimce shi fahimta ta gaskiya.

24. ‘Yan ta’adda suna karbar gudummawa daga hannun kafirai, da turawan yamma don su yaki ‘yan uwan su Musulmai. Duk wata kungiya ta ‘yan ta’adda wallahi zaka tarar da cewa, makiya Musulunci da Musulmai suna taimaka masu, suna basu gudummawa na kudi da makamai domin su rusa Musulunci. Babu wata jama’ah da zata yiwa gwamnatin ta tawaye, face sai ka tarar da cewa wasu makiya Musulunci da makiya wannan kasa suna goyon bayan su da basu taimako. Don haka ya zama dole gwamnati ta san da wannan. Domin babu yadda za’ayi ‘yan ta’adda suyi tasiri idan babu irin wannan goyon baya daga wasu kasashe.

25. ‘Yan ta’adda sune mafi sharrin halitta, kamar yadda Annabi (SAW) ya bayyana. Kuma Annabi ya kira su da karnukan wuta. Kuma Annabi yace idan ya same su, zai kashe su irin kisan da aka yiwa Aadawa. Kuma Annabi yace mafi alkhairi shine wanda ‘yan ta’adda suka kashe. Kuma Annabi yace za su ci gaba da bayyana lokaci-bayan-lokaci, kuma a duk lokacin da suka bayyana za’a murkushe su da karfin Allah.

Daga karshe, hanyoyi mafi sauki da hukumomi za su bi domin suyi maganin ta’addanci da ‘yan ta’adda sune:

1. Daukar matakin tuba, da komawa ga Allah, da yin komai tsakani da Allah, da hadin kai da yawaita Addu’o’i da rokon Allah.

2. Magance matsalar talauci, zaman banza, rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakanin matasa.

3. Samar da ababen more rayuwa da taimakawa jama’ah masu rauni.

4. Malamai su tashi tsaye wurin fadakar da al’ummah da karantar da su game da sharri da hadarin ta’addanci da ‘yan ta’adda ga Musulunci da Musulmai.

5. Gwamnati ta saukaka wa mutane hanyar samun ilimi, na addini da na zamani, domin rashin ilimi da jahilci suna haifar da samuwar ‘yan ta’adda a cikin al’ummah.

6. Gwamnati ta dauki kwararan matakai akan duk wani Malamin da yake yin wa’azin zuga mutane su dauki makami, suyi tashin hankali, ko suyi fito-na-fito da shugabannin su.

7. Matakin yin sulhu, da tattaunawa da lallashi, da ban hakuri.

8. Matakin Soja.

Ya Allah, muna tawassali da sunayen ka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka, kuma ka kawo muna karshen matsalar rashin tsaro da ya addabe mu a kasar mu.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author