Hukumar Tsaro ta SSS ta kasa gurfanar da Muhammad Kabir, mutumin da aka kama bisa zargin hadawa da kuma watsa bidiyon ‘hauragiyar auren Shugaba Muhammadu Buhari da Ministar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Jama’a, Sadiya Umar.
An samu cikas a Kotun Majistare ta Kano a ranar Laraba, lokacin da aka gurfanar da shi domin a fara sauraren tuhumar da za a yi masa. Maimakon a fara Shari’a, sai mai gabatar da kara, Iliya Bulus ya ce ya na neman a ba shi lokaci tukunna.
Ya shaida wa kotu cewa ya na so ya aika wa Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da fayil din binciken Kabiru, domin ya bada shawarwarin da suka dace.
Bulus ya ce a na su bangaren, su na yin duk wani abin da ya dace domin ganin sun nemi shawarwari daga Antoni Janar.
Lauyan Kabiru mai suna Ali Jamilu bai yi ja-in-ja din neman kada a dage shari’a ba. Sai dai kuma ya roki kotu ta sassauta sharadin belin da aka gindaya wa Kabiru, inda aka ce ya rika kai kan sa ofishin SSS na Kano a kowace rana.
Mai Shari’a ya amshi wannan roko, kuma ya amince. Ya umarci Kabir ya rika kai kan sa ofishin SSS a kowane sati sau daya tal.
Daga nan ya daukaka karar zuwa 24 Ga Maris, domin bai wa Antoni Janar na Jihar Kano samun isasshen lokacin da zai yi nazarin fayil din tuhumar da SSS ke wa Kabir.
Discussion about this post