Girmna da ake yi wa Najeriya kallon ta na da shi, har ake kiran ta ‘Giwar Afrika’ na neman komawa girman tubalin toka, idan aka yi la’akari da yadda bashi ya yi wa kasar katutu, har ya ke neman ya fasa mata ruwan ciki.
Wata kididdigar cin bashi da aka yi a tsakanin Najeriya, Angola, Afrika ta Kudu, Cameroon, Ghana, Cote d’Iviore da Rwanda, tun daga 2012 zuwa 2019, ta nuna cewa gwamnatin Najeriya ta ciwo bashi mai yawan kashi 44 bisa 100 na yawan basussukan da wadancan sauran kasashen suka ciwo.
Da aka koma batun bunkasar tattalin arziki kuwa, Najeriya ta zo ta biyar a cikin wadancan can jerin kasashe da aka dai lissafa a sama.
Saboda haka, a yanzu dai maganar ita ce, ba a wajen bunkasar tattalin arziki ne Najeriya ta ke ‘Giwar Afrika’ ba.
Najeriya ta zama giwar da tulin basussuka ya cika wa ciki ya kumbura, ta zama katuwa tamkar giwa.
Yayin da Bankin Bunkasa Kasashen Afrika (AfDB) ke hakikicewa da cewa bashin da ya kumbura cikin Najeriya ba abin tayar da hankali ba ne. AfDB na ganin cewa ko gishirin-Andurus Najeriya ta sha, zai iya sacce mata kumburin ciki.
Sai dai kuma Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya yi tulin bashin da Najeriya ta ci, abin tayar da hankali ne, wanda don an shekara ana jika kanwa ko gishirin-Andurus ana sha, ba magani za su yi ba.
NAJERIYA Da Cin Bashi: Ciwo Daban Magani Daban
Masana harkokin tattalin arzikin kasa da dama na ganin ba dabara, hikima ko azanci ba ne yadda Najeriya ta maida cin bashi kamar cin ’ya’yan itace a wajen biri.
Tsawon shekaru da dama, Najeriya ta dogara ne da ciwo bashi domin aiwatar da wasu muhimman ayyukan da ba ta da hanyar yin su idan babu wadatattun kudaden fetur, sai fa an ciwo bashi din.
Amma dai basussukan da Najeriya ta ci daga 2015 zuwa 2019, sun yi yawan da idan su masu bayar da basussukan ba su yi tunanin hanyoyin biya ba, to ya kamata mai karbar basussukan ta fara tunanin yadda za a yi a biya, ba tare da an koma ana kwasar dukkan dukiyar kasa ana amfani da ita wajen biyan bashi da kuma biyan kudaden ruwan dimbin bashin da ke hauhawa ba.
Har zuwa 1978, gwamnatin Najeriya ba ta bude ido da fita waje neman bashi ba, saboda yalwar danyen mai da aka samu a lokacin tsakanin 1972 zuwa 1973.
Sai bayan an shiga kunci ne a 1978, aka nemo ramcen dala bilyan 1 domin gudanar da ayyukan raya kasa.
To daga nan ne fa bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa dala bilyan 5.09.
Cikin Disamba, 1986, an kulla yarjejeniyar biyan bashi da Najeriya na dala bilyan 2.9, a cikin shekaru shida, sai kuma aka kara mata doriyar shekaru biyu a sama.
NAJERIYA: Giwa Ko Gauraka?
Basussukan da aka ciwo a baya aka yi wasu ayyukan raya tattallin arziki da su, a yanku masana’antun da aka gina da kudaden duk sun durkushe, ko kuma an durkusar da su.wasu daga cikin su, sun hada da Ma’aikatar Karafa ta Ajaokuta, Katsina Steel Rolling Mill, Jos Steel Mill, Delta Steel Compaya, Tashar Lantarki ta Iwopin, Aikin Samar da Ruwa na Adiyan da Aikin Tantance ’Yan Najeriya.
Maimakon a maida himma wajen bunkasa wadannan masana’antu, ana cin riba da su har a samu su biya basussukan nan, sai aka kashe su da gangan. A gefe daya kuma Najeriya ta yi kwance, sai juye-juyen ciwon ciki ta ke, yi saboda bashi ya cika cikin na ta ya yi tatil.
Sai da ta kai a cikin 2005, Shugaba Olusegun Obasanjo a wancan lokacin ya tattauna tare da shawo kan masu bin Najeriya bimbin basussuka, suka yafe mafi yawan lamunin ‘Paris Club’ har na dala bilyan 19.
Shin Me Aka Yi Da Basussukan Baya-bayan Nan?
Ofishin Kula da Basussuka na Tarayya ya ce ana bin Najeriya naira tiriliyan 26.2 ya zuwa karshen 2019.
Abin lura a nan shi ne, yayin da bashi ke karuwa, ya na hauhawa, a daya gefen kuma tattalin arzikin bay a karuwa ko kusa da irin yadda bashin ke hauhawa.
Sannan kuma a kullum duk wata cibiya hon hukuma ko kungiya ta haska fitila a cikin Najeriya, cewa ta ke yi fatara da talauci da kunci sai karuwa suke ta yi.
Gidan Talbijin na CNN ya fitar da kididdiga cewa kusan mutum milyan 87 ne a Najeriya ke rayuwar ya-zan-yi-ya-zan-yi-gobe.
Shin me ya sa a ke ci gaba da ciwo bashin da ba ya inganta tattalin arziki, kuma ba ya fitar da ’yan kasa daga cikin kangin talauci?
Rahoton BudgIT na 2019 ya tabbatar da cewa daga cikin kowace naira 100 da Gwamnatin Tarayya ke samu a matsayin kudaden shiga, to naira 60 na tafiya ne wajen biyan basussuka. Ana barin Gwamnatin Tarayya da naira 40 kacal. Har yau kuma gwamnati ba ta karyata wannan bayani ba.
Ma’ana, idan gwamnati ta samu kudaden shiga naira bilyan 100, to naira bilyan 60 na tafiya ne wajen biyan bashi a kowane wata.
Sannan kuma kasafin 2019 da na 2020 duk an samu gibin kusan naira tiriliyan 2 a 2019, sai kusan naira tiriiyan 3 a na 2020.
Zancen da manyan jami’an gwamnati ke yi cewa bashi ya na kara bunkasa tattalin arziki, to sai a tambaya a gani, wane arziki bashin da aka rika ciwowa a wadannan shekaru ya bunkasa?
A baya-bayan nan, kasafin kudi na fannin imi da kiwon lafiya sai raguwa ya ke yi.
Gwamnati ta kashe sama da naira tiriliyan 3 wajen gina manyan ayyukan raya kasar da ta ce za su samar da ayyuka ga mutum 79,000 kacal a bangaren ayyukan gine-gine.
Da dama na ganin har yanzu akwai harkalla da cuwa-cuwa sosai a wasu bangarorin ayyuakan da gwamnati ke aikwatarwa.
Saboda cikin 2019, an bayyana Najeriya ce ta 146 a jerin kasashen da ke da karancin cin hanci da rashawa da wawurar dukiyar kasa, a cikin kasashe 180.
Wannan ya nuna kenan kasashe 145 sun fi shugabannin da ke rike da madafun iko a Najeriya rikon amanar dukiyar jama’a kenan.
Discussion about this post