SATAR JARABAWA: Jami’ar jihar Kaduna, KASU ta kori dalibai 80

0

Shugaban jami’ar jihar Kaduna dake Kafanchan Ahmed Ahmed ya bayyana cewa jami’ar ta kori dalibai 80 da aka kama da laifin satar jarabawa a jami’ar.

Ahmed yace an kama wadannan dalibai da wannan laifi ne a zangon karatun ta shekara 2018/2020.

Ya fadi haka ne a bikin daukan sabbin dalibai da aka yi a harabar jami’ar dake Kaduna da Kafanchan ranar Laraba.

Ahmed ya ce abinda suka yi basu kyauta wa kansu ba bayan wahala da suka yi kafin su samu shiga jami’a.

“ Kamar yadda ake samun karuwar yawan dalibai a jami’ar ya zama dole jami’ar ta maida hankali wajenkawo karshen satar jarabawa.

“Dalibai 80 aka kama wannan laifi a zangon karatu na 2018/2019 inda 10 daga ciki suna karatu a Kafanchan.

Baya ga haka Ahmad yace jami’ar ta maida hankali wajen hana kungiyoyin asiri, ta’ammali da miyagun kwayoyi da sauran miyagun aiyukka a harabar makarantar.

Ya kuma hori sabbin daliban da aka dauka da su maida hankali a karatun su domin jami’ar baza ta yi kasa kasa ba wajen hukunta duk wanda ta kama yana wasa da karatun sa.

Daga nan mataimakin shugaban jami’ar Yohanna Tella yace bana jami’ar ta dauki sabbin dalibai 4,650 inda 700 daga cikin su za su yi karatu a Kafanchan ne.

Tella wanda ya wakilci shugaban jami’ar Muhammad Tanko a bukin ya yi kira ga sabin daliban kan maida hankali a karantun su a koda yaushe.
Sannan kuma ya yaba wa gwamnatin jihar Kaduna Karkashin gwamna, Nasir El-Rufai kan yadda ta maida hankali wajen inganta karatu a fadin jihar.

Share.

game da Author