Kashi 80% na wasu ‘yan Najeriya sun amince da sakamakon binciken da Kungiyar ‘Transparency Internarional (IT) ta yi cewa cin hanci da rashawa sun kara muni cikin 2019 a Najeriya.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da PREMIUM TIMES ta shirya, bayan fitar rahoton IT da ya nuna Najeriya na sahon farko Na kasashen da rashawa ta yi muni a duniya cikin 2019.
Kuri’ar Jin Ra’ayi da PREMIUM TIMES ta shirya ya nuna cewa mutane 4,922 sun jefa kuri’a a shafin jaridar na Twitter. An shirya jefa kuri’ar ce aka bai wa jama’a tsawon kwanaki bakwai
An kuma tsara jefa kuri’ar ta yadda babu yadda za a yi mutum ya jefa sau biyu ko sama da haka. Sai dai sau daya kawai.
An yi wa jama’a tambaya kamar haka: “Shin ka yarda da Rahoton Kungiyar IT da ta ce rashawa ta kara muni sosai a Najeriya, cikin 2019. Ka amsa da “e” ko “a’a.”
Mutane 3,760 (kashi 76.4) sun yarda da binciken ‘Transparency Internarional’. Mutane 1,162 (kashi 23.6) kuma ba su amince da binciken ba.
A cikin kasashe 180, TI ta ce Najeriya ta fi kasashe 145 lalacewar cin hanci da rashawa a duniya. Wannan sakamako ya nuna al’amarin yaki da cin hanci ya tabarbare kenan a 2019, ya ma fi na shekarar 2018.
Najeriya ta samu maki 26% 100% a awon daraja ko akasin haka da a binciken da TI ta gudanar.
A cikin kasashe 19 da rashawa ta yi wa illa a Afrika, Najeriya ta 4 a lalatattu, kamar yadda kungiyar CISLAC, wani reshe na TI ta bayyana.
Shugaban CISLAC, Auwal Rafsanjani, ya ce an yi wannan kirdadon bincike da bada maki ne a bisa irin kallon wuru-wurun da ‘yan Najeriya ke ganin ana tabkawa a hukumomin shige-da-fice, kwastan, Majalisar Tarayya, fannin shari’a, yadda cukumurdar hada-hada a Najeriya da kuma yadda ake samun shiga jami’o’i da kuma yadda ake daukar ma’aikata a kasar nan.
Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta kai amincewa da sakamakon rahoton da TI ta bayar.