Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta bayar da umarnin duk inda aka ga tsohon shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Dikko Inde.
Dikko ya yi shugabancin hukumar kwastan daga 2009 har zuwa 2015.
Kotu ta bada sammacin a kamo shi duk inda aka gan shi, saboda bijire wa umarnin kotu na ya kai kan sa da ya ki yi, ba sau daya ba sau biyu ba.
Hukumar ICPC ta maka su kotu, bisa zargin hada baki da wasu mutane biyu suka tafka harkallar wawurar makudan kudade.
Yayin da aka je kotu a ranar Litinin, lauyan Dikko mai suna Solomon Akuma, ya gabatar wa kotu da takardar shaidar rashin lafiyar da Dikko ya yi ikirarin ya na fama da ita.
Akuma ya ce Abdullahi Dikko na fama da matsanciyar rashin lafiya, wadda ta kwantar da shi yanzu haka a asibiti a London.
Sai dai kuma da Mai Shari’a ta koma ta kan lauya Akuma, ya tambaye shi cewa ya ce zai je da Dikko a ranar Litinin din, amma kuma ya je wa kotu da wani zance na daban.
Bayan wannan, Mai Shari’a Ojukwu ta yi nazarin rahoton shaidar rashin lafiya da lauyan Dikko ya kai, wadda wani asibiti mai zaman kan sa da ke kan titin Ahmed Musa, Jabi, Abuja.
Daga nan ta dubu lauya ta ce abin da takardar bayanan asibitin ta nuna, ba ta ce an kwantar da Dikko asibitin London ba.
Daga nan sai ta umarci masu gabatar da kara su jingine batun kamo shi tukunna, idan suka bincika suka gano tabbas ya na can asibiti a kwance.
“Amma idan ku ka gano ba gaskiya ba ne, to ku kamo shi ku kawo shi wannan kotun a ranar 16 Ga Maris.” Inji Mai Shari’a.
Tun bayan saukar sa shugabancin kwastan ne Dikko ke fama da tsomomuwar bincike, tuhuma da kwace masa kadarori masu tarin yawa da EFCC ta sha yi.
A yanzu kuma ana tukumar sa da wasu mutane biyu da yin haramben naira bilyan 1.1.
Cikin 2017 an kwace bargar wasu tulin motocin alfama masu tsaya sosai, a wani gida na sa, inda ya boye su a Kaduna.
Bayan wannan an kuma kwace baburan A Daidaita Sahu da sauran tulin kayan alatu.
Sannan kuma a cikin tangamemen dakin da boye wasu manyan darduma sama da 500 masu alfarma da aka shigo da su daga waje, an zakulo wani akwati da aka fasa aka samu kudaden kasashen waje,
kwatankwacin naira biliyan 1.5.
Duk gwamnati ta kwace wadannan a hannun sa.
Discussion about this post