SABON RIKICI: An kashe sojoji biyu, an kone bukkoki 150 a Filato

0

An kashe sojoji biyu tare da ji wa wani soja rauni, a wani harin kwanton-bauna da aka kai wa sojojin sintiri na ‘Operation Safe Heaven’ a yankin Barkin Ladi, Jihar Filato.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta tabbatar da kisan sojojin tare da jikkata daya, kamar yadda Kakakin Yada Labarai, Ubah Ogaba ya tabbatar.

Ya ce al’amarin ya faru ne kusa da Gidan Akwati, a Karamar Hukumar Barkin Ladi a cikin dajin yankin.

Wani da aka kone gidan sa mai suna Usman Adam, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, da farko bah aka kawai gabagadi sojoji suka shigo suka kone musu gidaje ba.

“Da farko sun dai zo da safe, suka kira mu mitin. Muka taru, aka zauna aka gana. Sai suka ce mana mu fiddo musu da duk wasu masu laifin da ke cikin mu.

“Bayan sun tafi, ba a dade ba kuma sai ga sojoji garke guda a kan motoci da babura. Su na zuwa sai kawai suka rika banka wa gidajen mu wuta.

“Mu duk ba mu san dalili ba, sai daga baya ake shaida mana wai an kashe musu soja biyu, kuma an raunata daya. Ni ma nan an kone gida na.”Inji Usman Adam.

Shi ma shugaban Fulanin yankin, Shu’aibu Bayero, ya ce “Ina tabbatar maka an kone gidaje za su kai 150 a rukunin yankuna hudu da sojojin suka dira.

An tambayi Kakakin Yada Labarai na ‘yan sanda, amma ya ce bai samu rahoton kone gidajen ba.

An yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘Operation Safe Heaven, amma bai daga waya ba.

Share.

game da Author