SABON LALE: Maryam Sanda ta daukaka karar neman soke hukuncin kisa

0

Maryam Sanda, matar da aka yanke wa hukuncin kisa sanadiyyar samun ta da laifin kashe mijinta, ta hanyar caccaka masa wuka, ta daukaka kara.

Ta daukaka karar hukuncin kisa ta hanyar rataya, wanda Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yanke mata a ranar 27 Ga Janairu, 2020 a Babbar Kotun FCT, Abuja.

Maryam ta daukaka karar ce a ranar Alhamis din nan, a Kotun Daukaka Kara ta Abuja.

Ta nemi a soke hukuncin kisan da kotu ta ce ta yi wa mijin ta mai suna Bikyaminu. An gurfanar da ita kotu tun cikin watan Nuwamba, 2017.

Lauyan Maryam da ya daukaka kara, ya ce mai shari’a Yusuf Halilu bai yi wa Maryam adalci ba ko kadan. Ya bada dalilan da ya ce su ne hujjar da aka kasa tabbatar cewa Maryam ta yi kisa, amma duk da haka aka yanke mata hukuncin rataya.

Hujjojin Maryam na rashin yarda da hukuncin kisa

1. Babu shaida ko kwaya wanda ya ce a gaban sa aka yi kisan.

2. An kasa gabatar wa kotu wukar da aka ce Maryam ta yi kisa da ita.

3. Babu sakamakon binciken gawa daga likita, wanda ya nuna cewa kashe Bilyaminu Maryam ta yi.

4. Bayanan shaidun da mutane biyu suka bayar, sun ci karo da juna.

5. Alkali Yusuf Halilu ya yi gaggawa da azarbabin yanke hukunci ta hanyar amfani da shaidun wane-ya-ji-ga-wane.

Lauyan Maryam, sanannen bababan lauyan nan ne, Ricky Tarfa. Ya gabatar wa Kotun Daukaka Kara Dalilai har 20 da ya ce sun nuna Yusuf Halilu ya yi babban kuskuren yanke wa Maryam hukunci.

Idan ba a manta ba, kwanan nan wasu kungiyo yi uku sun fito sun kalubalanci hukuncin ratayar da aka yanke wa Maryam.

Share.

game da Author