A wani rahoto da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayar ta shaida cewa jami’anta sun kashe mahara 17 sannan sun kwato dabbobi 189 a karamar hukumar Kankara.
Kakakin rundunar Gambo Isah ya sanar da haka ranar Alhamis.
“ A yau ranar Alhamis da misalin karfe uku na rana muka samu labarin cewa wasu mahara dauke da bindigogi kira AK 47 sun far wa kauyen Gurbi dake karamar hukumar Kankara.
“A kauyen maharan sun yi bata kashi da kungiyar ‘yan banga inda har suka kashe mutane 4 sannan sun kwashe dabbobin mutane da dama.
Isah yace nan da nan rundunar ta aika da jami’an ta domin kawo wa mutanen wannan kauye dauki.
” Bayan sun isa sai suka yi karo da maharan. Anan ne fa aka rika musayan harsashi a tsakanin su. Jami’an ‘yan sanda sun kashe mahara 17 Sannan wasu da dama sun arce da rauni a jikin su.
“ Mun kwato dabbobi 189 da maharan suka sace da suka hada da shanu 80, tumakai 108 da jaki daya.
Isah yace rundunar zasu yi farautar sauran maharan da suka tsere cikin daji.
Idan ba manta ba jihar Katsina wadda ita ce jihar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito daga na fama da hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
Ita kan ta garin Daura, mahaifar shugaba Buhari bata tsira ba domin a karshen shekarar da ta gabata aka shigo har gidan magajin garin Dauran aka yi garkuwa dashi.
Bayan haka kananan hukumomi da dama na fama da irin wannan ta’addanci daga mahara da kan far musu a ko wani lokaci.
Tsaro ya yi matukar tabarbarewa a yankin Arewa musamma yankin Arewa Maso Yamma.
Mutane da dama sun rika kira ga shugaba Buhari da ya canja shugabannin hukumomin tsaron Najeriya suna masu cewa dabara ta kare musu a yanzu, tunda suka kasa kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasar.
Discussion about this post