Hanan, ’yar Shugaba Muhammadu Buhari ta musanta zargin take hakki ga wanda ya sayi wani layin da ta taba amfani da shi a baya ya yi mata a kotu.
Anthony Okolie, ya maka Hanan kotu bayan da jami’an SSS suka tsare shi tsawon makonni 10 a kan hutumar sa da amfani da layin da ‘yar shugaban kasa ta taba amfani da shi.
Lauya Tope Akinyode ne ya shigar da kara a madadin Okolie wanda ya ke wakilta wajen shigar da kasa.
Okolie dain ya kai karar SSS, Hanan da kuma kamfanin MTN a kana bin da ya kira “tsarewa ba bisa sharuddan doka ba”.
‘Hanan Sai Ta Biya Ni Diyyar Naira Milyan 500’
Okolie ya na neman Hanan da SSS da kamfanin MTN su biya shi diyyar naira milyan 500 a matsayin ramuwar wuyar da ya sha a hannun SSS saboda tsare shi da ya ce an yi ba a kan yadda dokar kasa ta gindaya sharudda ba.
Da ta ke magana a Babbar Kotun Tarayya da ke Asaba, jihar Delta a ranar Laraba, Hanan ta ce ba za ta yi magana a kan wannan zargi ba, saboda babu wata bukatar yin magana a kai.
Hanan ita ma ta yi magana ne ta bakin lauyan ta ME Sheriff.”
Yadda Hanan Ta Harzuka Mai Shari’a
Mai Shari’a Nnamdi Dimgba a cikin fushi ya maida martani a kan matsayar da Hanan ta dauka ta bakin lauyan ta.
“Yanzu kai Shefiff me Hanan ke nufi da za ta ce ba ta ga wanin dalilin da za ta yi magana ba? Har wani ya zo har kotu ya zarge ki, sai ki ce ba ki da abin da za ki ce? Ko ma ta ce ni ban danne masa hakki ko ban ci zarafin sa ba, sai ta gagara fada?
“Kai Sheriff a matsayin mai kare ta har za ka iya furta haka a kotu? Me ka ke nufi ne Sheriff?”
Shi kuwa lauyan SSS mai suna EE Daobri, ya shaida wa Mai Shari’a cewa bai karbi takardun bayanan yadda lamarin yake da wuri a Abuja ba. Don haka bai kammala shirin shigar da bayanan sa a kotu ba.
Lauyan wanda ya yi kara ya shaida cewa jami’an SSS na ci gaba da bibiya da bimbinin wanda ya ke karewa.
Daga nan sai Mai Shari’a ya shaida wa lauyan SSS cewa, “Idan har gaskiya ne abin da ya fada, to ka shaida wa SSS su daina ci masa dunduniya.”
An dage karar zuwa ranar 3 Ga Maris.
Shi dai wanda aka samu da lambar, ya bayyana cewa kamfanin MTN suka sauar masa da layin, bayan Hanan ta daina amfani da shi.
Sannan kuma ya ce shi bai san ma wani ya taba amfani da lambar ba.