Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewarashin jituwan da ya cukuikuye gwamnatin Kano da fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi matsalace da ya shafi jihar da gwamnatin jihar amma ba hurumin sa bane.
Buhari ya bayyana haka ne a takarda da kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya fitar bayan ziyarar da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da wasu sabbin zababbun yan majalisar jihar suka kai wa shugaban kasan a Abuja.
Buhari ya ce ba zai iya saka baki akan wannan sabani ba saboda komai na gaban majalisar jihar a yanzu.
” Tunda majalisar jihar Kano ta sa baki a wannan magana ba ni da damar cewa komai domin dokar kasa ta riga ta fayyace komai dalla-dalla.
” Saboda haka muddun aka ce wani abu da ya shafi jiha na gaban majalaisar jiha kamar yadda yake yanzu a Kano bani da damar iya cewa komai akai. Haka dokar kasa ta ayyana.
A na shi jawabin, gwamna Ganduje ya shaida wa manema labarai cewa ya kawo wa shugaba Buhari wannan ziyara ne domin ya yi wa sabbin zababbun ‘yan majalisar jihar iso sannan ya sanar wa shugaban kasa matsayin da wasu ayyukan da gwamnatin sa ke yi suke.
Da ya ke amsa tambaya game da sabanin dake tsakanin sa da sarki Sanusi, Ganduje ya ce ana nan ana ci gaba da tattaunawa domin a samu maslaha.
Bayannan ya tunatar da mutane cewa yanzu jihar Kano na da manyan masarautu hudu ne ba kamar yadda aka sani a da.
Discussion about this post