RIKICI DA MAKIYAYA: Shugabannin al’umma sun haramta cin naman shanu

0

An haramta wa al’ummar yankin Uwheru ta cikin Karamar Hukumar Ughelli ta Arewa cin naman shanu ko sayar da naman ko sayar da shanu, sakamakon fusata da hare-haren da suka ce makiyaya ke kai musu.

Manyan yankin ne ciki har da Kwamishinan Harkokin Ilmin manya na Jihar Delta, Patrick Mouboghare a wurin taron.

Kuma ya na daga cikin wadanda suka rattaba hana mazauna yankin ci, sayarwa ko dillanci shanu ko naman su a yankin.

An zartas da wannan haramcin cin naman shanu ko girgin sa a ranar Asabar da ta gabata, a taron a manyan shiyyar Uwheru suka gudanar.

Majiya ta shaida wa jaridar Punch cewa, “Wannan doka ta harata cewa daga yau kada wanda ya kara kawo mana naman shanu a yankunan wannan shiyya da masarauta ta Uwheru.

“ Ba a yarda ko a lokacin bukin rufe gawa ko shagulgulan bukukuwan aure ko na murnar zagayowar shekara a ga wani ya yi hidima da naman shanu.

“Bai fa yiwuwa, ku na kashe mu sannan kuma ku yi tunanin za mu rika sayen shanun ku mu na ci, alhali fitinar ku ta hana mu zuwa gona mu noma abin da za mu ci.”

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Litinin cewa makiyaya sun kashe mutum 86 a yankin Uwheru cikin shekaru 12.

Baya bayan nan an ce an kashe mutane 14, abin da mazauna yankin suka zargi sojoji da daure wa maharan gindi.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa an fara samun kashe-kashe a yankin tun lokacin da Fulani masu yawa suka yi wa yankin dafifi tare da shanu masu yawa garke-garke.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Delta, Hafiz, ya bayyana cewa an yi wani rikicin da jami’ai suka tono gawarwakin mutane shida.
Daga nan ya roki jama’a su yi zaman lafiya da juna.

Share.

game da Author