RASHIN TSARO: Jadawalin yadda aka kashe mutum 245 cikin watan Janairu a Najeriya

0

Wannan adadi na mutum 245, wadanda aka yi wa kisan-gilla ne kawai, ba a hada da wadanda suka rasa rayukan su ta dalilin hadarin mota, gobara, fadawa ruwa.

Akalla mutum 245 aka kashe a Najeriya, a cikin watan Janairu, a hare-hare da kashe-kashen da jaridun kasar nan suka ruwaito a cikin watan na farkon sabuwar shekarar 2020.

Rahoton da Kungiyar Bincike ta Expat Insider Survey ta buga a karshen 2019 kuma ya nuna cewa Najeriya ce ta ukun a sahun farko na lalatattun kasashen da rashawa da rashin tsaro suka yi wa katutu a duniya.

Yayin da Fadar Shugaban Kasa ke ci gaba da karyata duk wani rahoto mai nuna matsalar da ke tattare da Najeriya, musamman tsaro da rashawa, ita kuma Majalisar Tarayya da ta Dattawa sun nuna damuwa sosai dangane da matsalar tsaro a kasar baki daya.

Banda yawan kashe-kashen da ke faruwa a yaki da ta’addancin Boko Haram a Arewa, ana ci gaba kuma da kara samun kashe-kashe sanadiyyar hare-haren mahara masu garkuwa da mutane da fadace-fadacen makiyaya da manoma.

Wannan ne ma ya sa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta gudanar da jerin gwanon lumana a ranar Lahadi, domin ta nuna damuwar ta a kan lamarin.

Jadawalin Kisan Mutane 245 Cikin Watan Janairu, 2020

2 Ga Janairu – Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda takwas yayin da suka nemi shiga garin Michika, Jihar Adamawa.

4 Ga Janairu – Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 23 a kauyen Tawari, cikin Karamar Hukumar Kogi da ke Jihar Kogi.

6 Ga Janairu – Akalla mutum 30 aka kashe a lokacin da wata nakiya ta fashe a kan wata gada a Gamboru, Jihar Barno.

An kashe sojojin ruwa guda hudu, lokacin da mahara a gefen tiku suka kai wa jirgin ruwan da suke ciki hari a yankin Neja Delta.

Sannan kuma an kashe sojoji hudu, cikin su har da babban soja daya, a wani hari da mahara suka kai musu a kauyen Gwarm, da ke cikin Karamar Hukumar Munya, dake jihar Neja, a lokacin da suke sintiri.

7 Ga Janairu – Wani jami’in dan sanda da ke gadin wani banki, ya bindige direba, dan bautar kasa (NYSC) da kuma wani mutum a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

A dai wannan ranar ce kuma aka banka wa wasu mutane biyu wuta suka kone kurmus a Calabar, bisa zargin su da yi wa mai shagon aski fashi da makami.

Sannan a wannan ranar mahara suka kashe wani mai suna Yasir Usman a jihar Katsina.

9 Ga Janairu – Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato sun tabbatar da kisan da aka yi wa mutum 12 a kauyen Kombun cikin Karamar Hukumar Mangu.

11 Ga Janairu – An kashe sojojin sama hudu a wani farmaki da mahara suka kai musu a Unguwar Yako, kuma da hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

14 Ga Janairu – Arangamar makiyaya da manoma ta yi sanadiyyar kisan mutum biyu a Sobe, cikin Karamar Hukumar Owan da ke Jihar Edo.

An kuma kashe sojojin ruwa hudu a Gbagira, Karamar Hukumar Ilaje, jihar Ondo. An kashe su ne yayin da suke kokarin ceto rayukan wasu ‘yan kasashen waje su uku da aka yi garkuwa da su.

16 Ga Fabrairu – Mahara sun dira Gummi a Jihar Zamfara, suka kashe mutane 29. Duk a ranar ce kuma mahara suka kai wa tawagar Sarkin Pataskum hari, suka kashe mutum biyar a kan hanyar Kanuna zuwa Zaria.

18 Ga Janairu – An kashe soja daya da Boko Haram hudu a yakin da aka yi a Ngala, Jihar Barno.

An kashe mazauna sansanin gudun hijira su 20 a cikin sansani su.

Kuma Boko Haram sun kashe sojoji hudu a Bama duk a wannan rana.

Haka kuma rikici ya barke ya yi sanadiyyar kashe mutane hudu a Igalamela-Odolu, cikin Jihar Kogi.

19 Ga Janairu – Barayi sun fasa bututun mai a Lagos, inda gobara ta tashi har ta kashe mutum biyar a Alimosho.

19 Ga Janairu – An nuno wani biidiyo da Boko Haram suka watsa ya nuna inda yaro ya kashe wani matashin da aka shaida wani Kirista ne da aka yi garkuwa da shi.

20 Ga Janairu – An kashe sojoji 17 kuma an tsere da wasu a wani gumurzu da Boko Haram sau biyu a ranar, a kan titin Bama zuwa Gwoza.

21 Ga Janairu – An kashe akalla sojoji takwas a yaki da Boko Haram a Kaga, jihar Barno. Boko Haram sun yi shigar ‘yan sanda, suka bude wa sojoji wuta.

A wannan ranar mahara sun kashe mutum hudu a Keana, Jihar Nasarawa. Kuma a ranar ce Boko Haram suka kashe Shugaban Kungiyar Kiristoci ta CAN na Karamar Humumar Michika, Lawan Andimi. Kuma mahara sun kashe mutum daya a Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina.

23 Ga Janairu – Boko Haram sun kashe mutum 10 a Dikwa, Barno. An kashe su a kauyen Lura, kusa da Dikwa.

24 Ga Janairu – Hasalallu sun kashe mutane biyu a Bayelsa, bayan garin Yenagoa, bayan da aka zage su da yin fashi ta POS.

25 Ga Janairu – Wadanda ake zargin Boko Haram ne sun tada bam a masallacin Gwoza, jihar Barno, suka kashe mutum uku, wasu da dama suka ji ciwo.

Kuma ‘yan bindiga sun kashe mutum 13 a kauyen Kwatas, cikin Karamar Hukumar Bokkos, jihar Filato.

A ranar kuma can a jihar Neja, mahara sun kashe mutum 11.

27 Ga Janairu – Wani mutum ya caccaba wa budurwar sa wuka ya kashe ta a Jihar Bauchi, saboda ta yi waya da wani saurayin na ta a gaban sa, a Jihar Bauchi.

29 Ga Janairu – Wani mai suna Kalu Ilum ya bindige matar sa a Etitiama Nkporo, cikin Karamar Hukumar Ohafia, jihar Abia. Shi kuma an banka masa wuta ya mutu a harin daukar wa budurwar fansa da hasalallun matasa suka yi masa rubdugu.

A ranar wasu da ake argin makiyaya ne sun kashe mutum biyu a kauyen Ovia ta Arewa Maso Gabas da ke jihar Edo.

30 Ga Janairu ‘Yan fashi da makami sun kashe Adebayo Mukaila, wani dan bautar kasa (NYSC).

Share.

game da Author