Dangane da yawan kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane da ake yi ba kakkautawa a kasar nan, PREMIUM TIMES HAUSA ta ji jama’a da dama fadin albarkacin bakin su dangane da munin lamarin.
Wani mai suna Aliyu Yusuf, wanda wakilin mu ya hadu da shi a wurin cin abinci a Abuja, ya hakikice cewa, “tabbas na yarda gwamnatin Buhari ta tsaida tayar da bama-bamai a garuruwan Arewacin kasar nan. Abin ya takaita a Barno da Yobe da Adamawa. A can din ma, da wahala ka ji an jefa bam.
“Amma a gaskiya idan aka koma bangaren garkuwa da mutane, to babu wani tinkahon da gwamnatin Buhari za ta yi, sai dai mu ce ta gaza kawai.
“Idan ka na so ka auna gwamnatin Buhari da ta Jonathan, to shi dai Buhari cewa ya yi babu tsaro a lokacin Jonathan. Muka yarda da shi, muka kuma zabe shi domin ya gyara lamarin.
“To amma ai duk da rashin tsaro a lokacin Jonathan, masoyan Buhari sun yi tattaki a kasa daga garuruwa daban-daban tsawon kwanaki zuwa Abuja.
“Yanzu kuwa bayan Buharin ya hau, duk wanda ya ce zai yi tattaki a kan titi a kasa, ko daga nan zuwa can ne, to sai dai mahaifiyar sa ta sake haihuwar wani – idan ba ta gama haihuwa ba, ko kuma idan ta na raye a duniya har yanzu.” Inji Yusuf.
Ya kara da cewa yankin da Buhari ya fito, wato Arewa maso Yamma, shi ne ya fi munin hare-haren garkuwa da mutane, kamar Zamfara, Katsina, Sokoto da Kaduna.
“Yanzun kuma abin ya na kara muni a jihar Adamawa, jihar da uwargidan Buhari ta fito. Ka ga kuwa wane tinkaho ko farfagandar tsaro wannan gwamnatin za ta yi mana?”
Discussion about this post