Akalla mutum 1,013 aka kashe sanadiyyar rikice-rikice da suka faru a yankin jihohin Neja-Delta a 2019.
Wata kungiyar bin diddigin tashe-tashen hankula a yankin, mai suna PIND ce ta fallasa wannan adadi, wanda ya ce ya haura wayan wadanda suka mutu cikin 2018 dalilin kashe-kashe a wurare daban-daban.
Rahpton ya bayyana cewa an kashe mutanen 1,013 a 2019 a adadin rikice-rikice har 416.
Am kashe su a rikice-rikicen rikicin gonaki, yawaitar manyan makamai a hannun ‘yan tayar da zaune tsaye da kuma fadace-fadacen siyasa da na ‘yan kungiyar asiri.
Jihohin Cross River, Delta, Edo da Rivers ne aka ci kashe mutane a 2019 a yankin. Barayi da masu fashi a ruwa, masu garkuwa da mutane, matsafa da ‘yan fashi da makami sun kashe mutum 444 a hare-hare 260 a ahekarar.
Yayin da matsafa da ‘yan kungiyar asiri suka kashe mutane 272 a arangama 78 cikin 2019.
A shekara ta 2018 mutum 546 kadai aka kashe a Neja Delta cikin tashe-tashen hankula 351.
Hanyoyi na biyu masu muni da aka kashe mutane a yankin, su ne tarzomar gungu-gungun matasa, a Edo, Delta da Rivers.
Fadan kabilanci ya ci rakuka 197, yayin da aka tabbatar da rahoton arangama 77.
Discussion about this post