RASHIN GIRMAMA IYAYE: Mata ta roki kotu ta raba aurenta da mijinta a Kaduna

0

A ranar Talata ne wata matan aure mai suna Maryam Usman ta maka mijinta a kotun Magajin Gari dake jihar Kaduna domin a raba aurenta da mijinta Haruna saboda baya girmama iyayenta da yake yi.

A zaman da kotun ta yi Maryam ta bayyana cewa Haruna baya girmama ta a matsayin matarsa duk da cewa tana iya kokarinta wajen zama mata na gari a garesa.

Maryam mazauniyar Zangon Aya a jihar Kaduna ta roki kotun da ta raba aurenta domin baza ta iya ci gaba da zama da mijin da baya ganin darajar iyayenta ba.

Ta kuma ce a shirye take ta maida wa Haruna Naira 50,000 din sa na sadaki da ya biya a shekarar 2018.

Sai dai kuma Haruna ya musanta duk abin da Maryam ta fadi a kotu ya ce duk shari ce, da karya take ta yankawa.

Ya ce ya amince ya saki Maryam tare da karban kudin sadakin da ya biya a kanta.

Haruna yace Naira 70,000 ne ya biya a kanta a wannan shekara ba Naira 50,000 ba.

Alkalin kotun Muhammad Adam-Shehu ya umurci Haruna da ya gabatar da shaidar da zai nuna cewa ya biya sadakin Naira 70,000 a mai makon Naira 50,000 akan Maryam a zaman da kotun za ta yi nan gaba.

Za a ci gaba da shari’ar ne ranar 3 ga watan Maris.

Share.

game da Author