Shugaban Riko na Hukumar EFCC ya sake jaddada cewa rashawa da aikata almundahana ne musabbabin barkewar cutar Coronavirus Chana, har ta bazu cikin kasashen duniya samacda 30.
Dama cikin makon da ya gabata ne a taron yaye jami’an EFCC sama da 200 a Kaduna, Magu ya bayyana a gaban Shugaba Muhammadu Buhari cewa “Na yi amanna cewa rashawa da cin hanci ne suka haddasa Coronavirus a duniya.”
A wannan karo kuma da ya ke kara jaddada matsayar sa, Magu bai tsaya kan cutar Coronavirus kadai ba, sai ya kara da cutar Ebola da ta zazzabin Lassa, duk y ace musabbabin su daya ne, wato daga rashawa da aikata almundahana suka faru.
Dakta Ko ‘Daftan’?
A wannan karo kuma Magu cewa ya yi ya na zaton wasu masu binciken kwayoyin cututtuka ne suka kirkiri kwayar cutar zazzabin Lassa da cutar Ebola,
“Wasu mugayen maketatan da keta ta ci zuciyar su da tunanin kwakwalwar su ne suka kirkiro cututtukan.” Inji Magu.
Haka dai Magu ya fada a Hedikwatar EFCC a ranar Laraba, a Abuja.
“E, ina nan a kan baka na da matsaya ta cewa wasu mugaye masu gurbatacciyar kwakwalwa ce suka kirkoro wadannan kwayoyin cututtuka.
“Kai ba ma Coronavirus kadai ba, hatta Ebola ma kirkiro ta aka yi, wani babban mugu ne ya kirkiro ta don kawai ya jajibo babbar matsala ya watsa, ta yadu a wata kasa.
“Babu babban dan almundahana kamar wannan kwakwalwar sa ta birkice, tunanin sa da dimauta, kamar wanda ya zauna a dakin bincike ya kirkiro kwayar cutar da za ta kashe mutum da uwan sa.
Maganganun da Magu ya yi na kwanan baya, da kuma na baya-bayan nan a kan salsalar Coronavirus dai sun jawo masa caccaka da tsangwama a soshiyal midiya.
An yi ta kallubalantar sa cewa ya yi wa mutane shiru, tun da shi dai ba likita ba ne.