RANAR MASOYA: An yi gargadi matasa su rika amfani da Kororo roba don kaucewa kamuwa da cututtuka

0

Sakamakon bincike ya nuna cewa kashi 34 bisa 100 na ‘yan Najeria ne ke amfani da kwaroro roba a duk lokacin da za su yi jima’i.

Hukumar gudanar da bincike NOIpolls, hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau (NACA) da kungiyar AHF ne suka gudanar da wannan bincike.

Da yake gabatar da sakamakon wannan bincike ranar Laraba a Abuja shugaban NOIpolls Chike Nwangwu ya ce an gudanar da wannan bincike ne domin wayar da kan mutane mahimmancin amfani da kwaroron roba musamman a wannan lokaci da ake bukin ranar Masoya.

Nwangwu ya bayyana cewa kashi 82 bisa 100 na wadanda suka yi bincike a kai sun yarda cewa yana da mahimmanci a rika amfani da kwaroro roba a duk lokacin da za a sadu. Sai dai kashi 34 cikin wannan adadi sun ce lallai suna amfani da kwaroro roba a duk lokacin da za su sadu da mace.

Bayan haka shugaban hukummar NACA Gambo Aliyu ya bayyana cewa sakamakon wannan bincike zai taimaka wa gwamnati wajen toshe gibin rashin samaun kwaroro roba da ake fama da shi.

Aliyu ya kuma ce sakamakon zai taimaka wajen tsara sabbin hanyoyin dakile yaduwar cututtuka musamman cutar kanjamau.

Ya ce hukumar za ta ci gaba da wayar da kan mutane sanin mahimmancin amfani da kwaroro roba a duk lokacin da za su yi jima’i.

“Ba karuwanci ko kuma fasikanci muke tallatawa ba, burin mu shine samar wa mutane damar kare kansu daga kamuwa da cututtuka.

Darektan shirye-shirye na kasa na kungiyar AHF Echey Ijezie ya ce kungiyar za ta raba kwaroro roba kyauta guda 250,000 a taron ranar kwaroro roba na kasa da kasa na shekarar 2020.

Ijezie yace yin haka zai taimaka wajen samun ragowa daga cikin miliyoyin mutane dake fama da rashin samun kwaroro roba a Najeriya.

Ya ce tun daga shekarar 2011 kungiyar AHF ta fara raba kwaroro roba sannan zuwa yanzu ta raba sama da miliyan takwas.

Share.

game da Author