PDP ke yi wa Buhari zagon kasa da ingiza mutane su yi masa bore – Fadar Shugaban Kasa

0

Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana sakon fadar gwamnati a wata takarda da ya raba wa manma labarai.

Shehu ya ce tuntuni suka gano cewa jam’iyyar adawa ta PDP ta na shirya wa wannan gwamnati makarkashiya ciki harda zuga mutane su yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bore a Maiduguri.

” Wannan garagadin ya zama dole domin samyn labarin da muka yi cewa an yiwo hayan wau mataza har 2000 domin su yi zanga-zangar a kori manyan hafsoshin sojin Najeriya a Abuja ranar litinin.

” Bayan haka ita jam’iyyar PDP da mabiyanta suna garzayawa ofisoshin jakadun Najeriya domin yin zanga-zangar nuna rashin amaincewa da salon mulkin shugaba Buhari.

” Sannan kuma mun damu labarin cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ke amfana da Boko Haram suna nan suna ta hayan mutane domin fitowa yin wannan zanga-zanga da suke shirin yi.

Shehu ya kara da cewa babi abinda wadannan yan siyasa suke burin su gani shine yadda za a tozarta gwamnatin Buhari. ” Amma kuma asirin su ya tonu tun yanzu domin ko a ziyarar Buhari jihar Barno, dubban mutane ne suka yo gungu-gungu suka tarbe sa cikin kwanciyar hankali da murna kafin aka ci karo da wadanda ‘yan adawa suka yo haya domin su yi masa ihu.”

Share.

game da Author