Hukumar Hana Ma’aikata Cin Rashawa ta ICPC, ta bayyana a shafin ta na twitter a ranar Talata cewa ta buga neman ma’aikata 220, amma ya zuwa yanzu an samu matasa har 361, 631 wadanda suka cika fam.
Sai dai kuma hukumar, wadda ke yaki da cin hanci, rashawa da wawuran kudade a cikin ma’aikatan gwamnari, ta bayyana cewa ba za ta dauki kwashi-kwaraf ba, sai wadanda ke da sakamakon da ake bukata, kuwa wadanda suka cika sharuddan da Hukumar ICPC din ta gindaya.
“Za a dauki kwararru a fannin aikin Akawu, Shari’a, Tattalin Arziki, Fasahar Kwamfuta, Nazarin Bincike da Kwamfuta, Kimiyyar Kwamfuta, Kididdiga, Lissafi, Aikin Jarida, Safiyo, Injiniya da Bin-diddigin-kwangiloli.”
ICPC ta ce bayan an gama daukar wadanda suka cancanta, za kuma a zo a yi wata jarabawar gwajin iya aiki, ta sanin halayya da kuma tantance wanda za a dauka ta hanyoyin da suka hada har da tabbatar da inganci da sahihancin takardun karatu da na jarabawar sa.
Duk wannan cike-cike da bin-diddigin yin tankade da rairaya, ba shi kenan ba, domin ICPC ta ce dukkan wanda za a yi wa gwajin cancanta zai ga takardar bayanan da zai cika ta sakon kar-ta-kwana daga kamfanin tuntuba na DCSL Corporate Services, Ltd.
A karshe kuma ICPC ta ce za a yi wa wadanda aka tantance horon aikin jami’an tsaro na motsa jiki, tsawon watanni shida, domin a kara tabbatar da cewa duk wanda za a dauka, to ya kasance lafiya garau ya ke.