Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf domin bude wurin gwajin cutar ‘Corona Virus’ a asibitin koyarwa na Jami’ar Legas.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya sanar da haka a shafin sa na tiwita a yanar gizo.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne hukumar ta sanar cewa ta bude wuraren gwajin cutar zazzabin lassa guda biyar a fadin kasar nan.
Asibitin koyarwa na jami’ar Legas na daya daga cikin wadannan wurare da hukumar ta bude sannan kuma ta kashe Naira miliyan 100 wajen zuba ingantattun kayan aiki na zamani.
Ihekweazu ya ce a yanzu haka kwayoyin cutar Coronavirus ya fara kareda kasashen duniya inda ya zama dole a bude wuraren gwajin cutar a kasar nan.
“ Za a bude wurin yin gwajin cutar a Legas da Abuja mahimmanci wadannan garuruwa da kuma nan a ke samun yawa-yawan masu shigowa da fita daga kasar nan.
Ihekweazu ya ce hukumar ta tsaron hanyoyin ganowa da dakile cutar sannan ta hada hannu fannin kiwon lafiya na tashohin jiragen sama da ruwa domin ganin an hana shigo da cutar kasar nan.
Ya yi kira ga matafiya da su gaggauta kiran wadannan lambobin waya 0800-970000-10 da zaran sun fara zazzabin ko rashin iya numfashi yadda ya kamata bayan kwanaki 14 da dawowar su daga kasar Chana.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Amma ita cutar Corona Virus sabuwar cuta ce da ba a taba samun ta a jikin mutum ba.
Ita cutar akan kama ta ne a dalilin cudanya da dabbobi domin sune ke dauke da ita. Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin muamula da dabbobi na gida da na daji.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
An samar da wasu hanyoyi na gaggawa domin kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
WHO ta yi kira da a rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.