Najeriya na yunkurin dakatar da shigo da kifi nan da 2022

0

Ministan aiyukkan Noma Sabo Nanono ya bayyana cewa gwamnati daga shekarar 2022, gwamnati zata dakatar da shigo da danyen kifi daga kasashen waje kamar yadda ake yi yanzu.

Minista Nanono ya fadi haka ne da yake jawabi a dakin taro na ma’aiakatan Noma a likacin da kungiyar masu kiwon kifi na Najeriya (NFAN) suka kawo masa ziyara a a Abuja.

Ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta dauki matakan da za su taimaka wajen raya fannin kiwon kifi saboda koda a gaba za a rika fita da kifi daga Najeriya zuwa kasashen waje ana saida wa kamar yadda ake shigo da su yanzu.

Nanono yayi kira ga kungiyar da ta mara wa gwamnati baya domin ganin hakan ya tabbata.

A nashi jawabin, shugaban kungiyar Gabriel Ogunsanya ya yaba kokarin da ministan ke yi wajen inganta aiyukkan noma a kasar nan.

Ogunsanya ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen farfado da fannin kiwon kifi musamman ta hanyar sama wa masu kiwon kifi jari. Sannan kuma da inganta bincike domin sanin yadda za a iya kiwon kifi a kasar nan musamman irin wadanda ba a kiwon su a Najeriya.

Daga nan sai Ogunsanya ya bayyana cewa kungiyar na kokarin ganin ta hada kan duka manoman kifi dake sana’a a kasar nan.

Share.

game da Author