Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar cewa Najeriya da wasu kasashen Afrika biyar sun bude wuraren gwajin cutar Coronavirus a kasashen su.
An bude wuraren a kasashen Senegal, Afrika ta Kudu, Ghana, Madagascar, Sierra-Leone da Najeriya.
WHO ta ce ta tallafa wa wadannan kasashe ne ta hanyar samar da wuraren gwajin cutar saboda yadda cutar ke kara yaduwa a kasar Chana da wasu kasashen duniya.
Kungiyar ta jinjina kokarin da kasashen shida suka yi wajen samar da wuraren gwaji a kasashen su.
Domin inganta hanyoyin dakile cutar shugaban WHO dake kula da yankin Afrika Matshidiso Moeti ya ce kungiyar za ta aiko da kayan gwajin cutar wadannan kasashe.
Akalla dala milyan 675 ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke bukata cikin gaggawa, domin yin ayyukan tallafin a kasashen da ke da raunin tsarin kiwon lafiya a fadin duniya, domin gujewa daga kamuwa da cutar ‘Conornavirus’.
Babban Daraktan WHO, Tedros Ghebreyesus ne ya bayyana haka da ya ke wa duniya jawabi a ranar Laraba, a Geneva, a hedikwatar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Ya ce cutar coronavirus ta zama annoba a duniya, wadda a daidai lokacin da ya ke jawabi ta bulla a kasashe 25 banda China.
Tedros ya ce a kasar Chana dai mutum 24, 363 sun kamu da cutar, ya zuwa lokacin da ya ke jawabi.
Ya kara da cewa kashi 99 bisa 100 na wadanda kan nuna alama, idan aka gwada su, akan tabbatar da cutar a jikin su.
“A sauran kasashe banda Chana kuwa, an samu adadin mutum 191 da suka kamu da cutar ta Coronavirus.
“Har zuwa ranar Laraba dai ba a samu sahihin rahoton bullar cutar a wata kasa ko daya cikin Afrika ba. Sai dai zargi da rahotanni marasa tabbas kawai.
Discussion about this post