NAIRA BILYAN 208.8: Yadda Zenith Bank ya ci mahaukaciyar riba a 2019

0

Bankin Zenith ya bayyana cewa ya samu riba ta zunzurutun kudade har naira bilyan 208.8 a cikin 2019.

Sanarwar da bankin ya fitar a karahen makon nan, ya bayyana cewa ya samu ribar naira bilyan 243 a cikin 2019, amma ribar ta koma bilyan 208.8, bayan cire harajin da ake biya ga gwamnati.

Wannan ne karo na farko a tarihin kafa harkokin hada-hadar bankuna a kasar nan, da aka samu riba a wani banki daya tal da ta haura naira bilyan 200.

Cikin 2018 dai Bankin Zenith ya samu ribar naira bilyan 232, bayan biyan haraji kuma kudin ribar ya rage saura naira bilyan 193.

Shugabannin bankin sun ce akalla Bankin Zenith ya na da kadarori da jarin da jimillar adadin su ya kai naira tiriliyan 6.35.

Sun ce kadarori da jarin bankin ya karu idan aka kwatanta da yawan su a shekarar 2018 a naira tiriliyan 5.96.

Daga nan sun yi sanarwar cewa za a raba ribar bankin a kan naira 2.80 ga kowane hannun jari daya.

Yayin da ake kukan matsin tattalin arziki da kuncin rayuwa a cikin al’umma akalla milyan 87 a Najeriya, sai ga Bankin Zenith ya samu gagarimar riba a cikin wannan shekara.

Shi ma attajiri Aliko Dangote, ya kara samun tagomashin nasibin ciniki a 2019, inda likkafar ta kara yin gaba daga lamba 42 ya koma na 23 a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya.

Share.

game da Author