NAFDAC ta kama ganyen Wiwi tan 10.5 a Maiduguri

0

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC) reshen jihar Barno ta kama tan 10.5 na ganyen wiwi a Maiduguri.

Hukumar ta ce an boye wannan ganye ne a wani gidan ajiya dake jihar.

Shugaban hukumar Muhammad Abdullahi ya ce hukumar ta kama wasu mutane biyu da ake zargin su da hannu a boye wiwin a wannan wuri.

Idan ba a manta ba a watan Agustan 2019 ne Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa, ta kona kwantina 58 ta Tramadol da sauran muggan kwayoyi har na naira bilyan 14 da milyan 700,000.

Shugaban hukumar Hamid Ali ya ce an kona magungunan ne a karkashin Kwamitin Kwastan na Kone Muggan Kwatoyi tare da hadin guiwar sauran hukumomin hana safara da tu’ammali da muggan kwayoyi.

Ali ya yaba wa irin kokarin da sauran hukumomin irin su NAFDAC da NDLEA me yi wajen dakile muggan kwayoyi a kasar nan.

Ya ce jajirtaccen aikin hana shigo da kwayoyi da Kwastan ke yi da kuma hana tu’ammali da ita da NDLEA da NAFDAC ke yi, aiki ne na ceto rayuwar al’umma da kuma sadaukar da kai saboda su.

Share.

game da Author