Mutuwa ta sake ratsa Majalisar Dattawa, ta dauki Sanata

0

An tabbatar da rasuwar Sanata Ignatius Longjan da aka bayyana rasuwar sa a safiyar Lahadi.

Sanata Longjan mai wakiltar Shiyyar Filato ta Kudu, a karkashin jam’iyyar APC, ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiyar da ba a bayyana irin ta ba na tsawon lokaci.

Wani Sanata ya tabbatar wa PREMIUM TIMES rasuwar, amma ya ce kada a bayyana sunan sa, domin Shugaban Majalisar Dattawa ne ke da ikon bayyana rasuwar sanata a kasar nan.

“Amma an tabbatar Sanata Longjan ya rasu, domin an sanar da mutuwar sa a cikin wani guruf na mu na soshiyal midiya. Sai dai kuma ba mu bayyana ba, saboda Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ne ya kamata ya yi sanarwar.”

Ya ce sanatoci na ta aikawa da sakonnin ta’aziyya, jimami da alhinin rashin sa, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Lura da Al’adu da Bude Ido.

Longjan ya rasu ya na da shekaru 75 a duniya. Shi ne ya maye gurbin Sanata Jeremier Useni a zaben 2019.

Ya taba rike mukamin mataimakin gwamnan Jihar Filato daga 2011 zuwa 2015.

Idan ba a manta ba, watanni biyu da suka gabata, wani sanata mai suna Ben Uwajumugwu ya rasu. Sanata Ben na wakiltar jihar Imo ne kafin rasuwar sa.

Share.

game da Author