Kotun Koli ta tsige gwamnan jihar Bayelsa na jam’iyyar APC a zamanta ranar Alhamis.
A hukuncin kotun wanda maishari’a Ejembi Eko ya karanta ya bayyana cewa duka Alkalai biyar da suka yi nazarin karar sun amince da wannan hukunci da kotun ta yanke.
Dalilin tsige sabon gwamnan Lyon David na jam’iyyar APC shine samun mataimakin sa Biobarakuma Degi-Eremienyo da laifin mika wa hukumar zabe takardun karatun sa na karya.
A dalilin haka Kotun ta bayyana cewa wannan matsala ta shafi gwamnan tunda shine ya mika a matsayin mataimakinsa a lokacin zaben gwamnan jihar.
Daga nan sai maishari’a Eko ya umarci hukumar ta bayyana wanda ya zo na biyu a zaben gwamnan jihar sannan a rantsar da shi ranar Juma’a.
Wannan hukunci na kotun koli ya yi wa jam’iyyar APC yanka baya domin hatta shugaban kasa ya shirya tsaf domin halartar bukin rantsar da sabon gwamnan jihar.
Discussion about this post