‘Mun kasa gabatar da bayanan kashe kudade saboda mai bin-diddigin kudin ya makance’ – Jami’ar Badun

0

Jami’ar Ibadan ta bayyana dalilin ta na kasa gabatar wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya (AGF) bayanan binciken yadda ta kashe kudaden da gwamnati ke ba ta, tsawon shekaru hudu, saboda makancewar mai binciken kudin.

Micheal Alatishe, wanda shi ne babban mai kula da hada-hadar kudaden jami’ar, ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai kula da yadda Hukumomi ke kashe kudaden da gwamnati ke ba su.

Rabon da Jami’ar Ibadan ta bayyana wa gwamnati yadda ta ke kashe kudaden ta, tun 2014.

An Kama ‘Biri’ Sarkin Wayau

Sai dai kuma mamaki, al’ajabi da ta’ajibi ya kama mambobin kwamitin, yayin da suka gano cewa ko a shekarar da ta gabata sai da aka biya mai bin-diggigin kudaden ladar aikin sa na shekarar da ta gabata, sai suka harzuka, suka ce a gaggauta kafa kwamitin bincike a gano inda kullin harkallar ya cukurkude.

Shugaban Kwamiti Oluwale Oke, ya bayyana cewa babu yadda za a yi don mai bin-diddigin kashe kudade ya makance a ce wai babu sauran wani mai aiki a kamfanin, idan ma har makancewa din ya yi da gaske.

Sannan kuma Oke ya yi mamakin yadda aka biya “makaho” kudin aikin shekarar da ta gabata, wanda bai yi ba, domin an ce ya makance.

“Kai ni fa ban yarda ba a ce cibiyar ilimi kamar Jami’ar Ibadan ta ce wai saboda makantar wani mutum dayw a ne ya hana ta gabatar da bayanan kididdigar yadda ta ke kashe kudaden da ake ba ta, tun 2014 har yau.”

Daga nan ya yi wa Alatishe hargagin cewa “tunda kun kasa gabatar da bayanan kashe kudaden ku, to na za mu bari gwamnati ta ba Ku kudaden kasafin ayyukan wannan shekarar ba.”

Share.

game da Author