MUMMUNAN HARI: Yadda Boko Haram suka kashe matafiya 20 kusa da shingen tsaron shiga Maiduguri

0

‘Yan ta’addar Boko Haram sun kai mummunan hari a kan matafiyan da sojoji suka hana shiga cikin Maiduguri.

An tabbatar da cewa sun kashe mutane 20, ciki har da kananan yara, sannan kuma sun arce da wasu matafiyan masu yawa.

Mummunan harin ya faru ne a garin Auno, kusa da shingen tsaro da sojoji suka kafa, kilomita 24 kafin shiga Maiduguri daga Damaturu.

Sojoji sun kafa dokar hana matafiya shiga Maiduguri tun daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe.

Hakan ya sa duk matafiyan da ba su wuce shingen kafin karfe 6 na yamma ba, to sai dai su kwana kusa da shingen tsaron, wanda sojoji suka yi kaka-gida a wurin.

Matafiyan da Boko Haram suka kashe sun yada zango ne a garin Auno da ke kusa da shingen sojojin, da nufin idan an bude hanya washegari karfe 6 na safiya, sai su shiga cikin Maiduguri.

Sai dai kuma sun hadu da tsautsayin harin Boko Haram, inda wajen karfe 10 na dare a ranar Lahadi, aka bude musu wuta lokacin da su ke cikin motocin su su na barci.

Gwamna Babagana Zulum da kan sa ya je gani-da-ido a garin na Auno, a safiyar Litinin.

Wani jami’in gwamnarin Barno ya shaida wa wakilin mu cewa da idon sa ya ga gwarwakin fasinjoji suna cin wuta a cikin mota, kuma har da gwarwakin kananan yara.

Wani da al’amarin ya faru ya na garin ya shaida wa wakilin mu cewa Boko Haram sun kone gidaje 18, kuma sun gudu da wasu mutane da dama.

Malam Yunusa kuwa ya ce ya ga wasu gawarwakin kwance a kasa, sannan kuma ya kirga motoci 18 da Boko Haram suka cimma wa wuta.

Har zuwa lokacin da Gwamna Zulum ya isa wurin, wasu motoci na ta cin wuta.

Share.

game da Author